Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar rashin isassun muhallai a Najeriya
- Marubuci, Abdou Halilou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
A kasashen duniya da dama al'ummomi na fuskantar matsalar rashin matsugunai.
Wannan ya kasance babban lamari ga gwamnatocin kasashe game da tsare-tsarensu na wadatar da jama'a da gidaje masu nagarta da inganci a yankunan birane da na karkara.
A nahiyar Afirka, Najeriya ta kasance kan gaba wajen yawan al'umma, sai dai duk da kasancewarta kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka, tana fuskantar irin wannan matsala kamar sauran kasashe marasa karfin tattalin arziki.
Zuwa yanzu dai ana iya cewa Najeriya ta gaza samar da isassun matsugunai ko gidajen kwana domin gudanar da rayuwa irin ta masu matsakaicin hali ga miliyoyin al'ummarta.
Kididdiga ta nuna cewa ana karancin gida a Najeriya da yawansu ya kai kimanin miliyan 22.
A wata hira da BBC, Shugaban bankin bayar da lamunin gina gidaje na Najeriya Arc. Ahmed Dangiwa ya ce "kashi 80 cikin 100 na 'yan Najeriya ba sa iya gina gida ko kuma su fitar da kudi su saya."
Haka nan matsalar na kara munana da karancin gida 900,000 a kowace shekara.
A kan haka ne Najeriya ta kafa wani banki mai suna Federal Mortgage Bank, wanda ke bayar da lamunin gina gidaje ga al'umma.
A wasu kasashen gwamnati na daukar nauyin gina gidaje kyauta ga masu dan karamin karfi a yayin da wasu kasashen ke gina dumbin gidaje ba tare da sun tsawwala kudi ba domin sayarwa al'umma cikin sauki.
Mazauna birane a kudancin Nijeriya kamar sauren birane a sauran bangarori na kasar na fuskantar matsalar rashin wadatattun gidaje ga al'umma.
A cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar gaban Majalisar kare hakkin Dan Adam da ke Geneva, ya nuna ire-iren nau'in matsalolin da ke tattare da rashin gidaje wadatattu ga jama'a.
Rashin gidaje na haddasa matsaloli daban-daban a cikin rayuwar al'umma, kama daga na tattalin arziki da bunkasar rayuwa da ci gaba mai daurewa da dai sauren su.
Miliyoyin mutane ne aka kora daga unguwannin talakawa a cikin shekara 20.
Kuma akasari ma sanarwar da ake ba su 'yar kadan ce game da wa'adin da ake basu na su bar unguwannin ko kuma gidajen.
Ko a bara, jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan samar da gidaje Leilani Farha ta bayyana cewa fiye da kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na zaune ne a gidaje irin na marasa karfi gami da rashin abubuwan more rayuwa.
Hakan na faruwa ne ba tare da an tanadar masu wani wuri ba a madadi wurin da a baya suke tsugune.
Najeriya dai na da dumbin kungiyoyi na kwararru ta bangarori daban-daban da kan iya taimakawa wajen samar wa al'ummar kasar gidaje.
Ire -iren wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyar masu kula da tsara birane da kungiyar masu kula da ingacin gine gine da dai sauren su.
Sai dai matsaloli da dama su na hana ruwa gudu a cikin lamarin .
Da dama daga cikin al'umma ba za su iya mallakar gidajen shiga ba duk tsawon rayuwarsu a duniya sabili da matsaloli da dama na rashin wadata da tattalin arziki da suka addabe su.