Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar rashin isassun gidaje a Najeriya ta munana - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Najeriya na fama da matsalar karancin gidaje da yanayin da ke sahun kasashen da lamarinsu ya fi muni a duniya.
Fiye da kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na zaune ne a gidaje irin na marasa karfi gami da rashin abubuwan more rayuwa kamar yadda jami'ar MDD da ke sa ido kan samar da gidaje Leilani Farha ta bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ta tana wadannan bayanai a Abuja babban birnin kasar, yayin da ta kawo karshen wata ziyara ta kwana 10 da ta yi, don binciken yanayin gidaje a manyan biranen kasar.
Ms Farha ta ce "Al'amarin gidaje a Najeriya na cikin mummunan yanayi. Zai yi wahala tsare-tsaren da ake da su a yanzu su iya magance babbar bukatar gidaje da ake da ita
"Ana ci gaba da samun karuwar muhallan da ba su da tsari inda yanayin ke azabtar da mutane, kuma tabbas hakan na daga cikin mafi muni a duniya."
Ta kara da cewa wasu muhallan ba sa samun ingantaccen ruwan sha da bandakuna da kuma wajen zubar da shara - kuma da yawan mutane na cikin hadarin kamuwa da cututtuka saboda yadda suke rayuwa kusa da gurbataccen ruwan da ba ya tafiya inda kwayoyin cuta ke yaduwa.
Ana sa ran yawan al'ummar Najeriya zai nunka sau biyu zuwa miliyan 400 a tsakiyar karnin nan, kuma dama tuni kasar ce mafi yawan mutane a nahiyar Afirka.
Mutum miliyan 22 ba su da muhallai a kasar, wacce take a yammacin Afirka.
Rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ya tursasa wa mutum miliyan biyu tsere wa daga gidajensu, kuma hakan na kara munana lamarin rashin gidajen.
Ms Farha ta ce cin hanci da rashawa da ya shiga bangaren gidaje ya jawo ana ta gina gidaje na gani na fada da suka fi karfin mallakar mafi yawan 'yan Najeriya.
Ta kuma soki tsare-tsaren da ake da su a bangaren gidaje da ta ce ba su da kyau, da kuma yadda hukumomi ke amfani da karfi da wajen korar wasu al'ummu daga muhallansu, wadanda mafi yawa mata ne da yara.
Jami'ar ta MDD ta ce: "Ana bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana dakatar da fitar da mutane da ake yi daga muhallansu, har sai an samar da isasshiyar mafita da take kan tsari, domin tabbatar da cewa fitar da mutane da ake yi ya yi daidai da dokar kasa da kasa kan hakkokin dan adam."
Karin labaran da za ku so ku karanta