Matsalar tsaro ba laifin sojin Najeriya ne ba - Janar Magashi

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan harbin da aka yi wa masu zanga-zangar da ba sa ɗauke da makamai yayin zanga-zangar EndSARS.

Ministan tsaron ƙasar, Janar Bashir Salihi Magashi ne ya bayyana haka - ko da yake bai yi wani ƙarin haske ba - yayin wani taron manema labarai da ministocin ƙasar gami da hafsoshin tsaron Najeriya ranar Litinin a Abuja.

Lamarin da ministan ke magana a kai ya faru ne a ranar 20 ga watan jiya a Lekki Tollgate cikin jihar Legas.

Editanmu BBC Aliyu Tanko ya gana da ministan tsaron.

BBC: Wasu na ganin gazawar jami'an tsaro ta jawo wannan halin rasahin tsaro da ake ciki a Najeriya.

Janar Bashir Magashi: Wadanne jami'an tsaro ne za a dora wa wannan nauyin? Kai ka san tun shekaru 11 da suka gabata mu sojoji muke fagen daga a yankin arewa maso gabashi da na kudu maso gabashin Najeriya, da kudu maso kudu, kai har ma da kudu maso yammaci. Mun sha gaya muku cewa ba laifin sojoji ba ne.

BBC: Amma mutumin da ke zaune a wasu yankuna na jihar Katsina ko kuma Zamfara, ya ji ana cewa babu gazawar jami'an tsaro, yana iya cewa ba ka yi daidai ba.

Janar Magashi: NI ba zan taba cewa babu laifin jami'an tsaro ba. Kowa yana da na shi laifin. mU laifinmu shi ne ba a bamu abubuwan da za mu ce idan mun yi za mu gama aikin nan ba.

BBC: Kana nufin gwamnati ba ta ba da isassun kuɗi?

Janar Magashi: A'a. Gwamnati ta ba da komai. Janar Buhari ba abin da ba ya mana don nu sami nasarar abin da muke yi. Abin da nake nufi shi ne idan da kowa zai bayar da gudunmawa. Mutumin ƙauye idan ya ga ana abin da ba daidai ba ya kawo rahoto. Amma sai ka ga sai abu ya lalace sannan ake sanar da mu. Kamar a yankin arewa maso gabas, kananan hukumomi kusan 18 suka kwace, amma duk yanzu suna hannun mu.

BBC: Amma mutumin Baga ko na Kukawa idan ka fada masa haka zai ce akwai gyara a maganar ka.

Janar Magashi: To ai dama dole a sami gyara. Ka taba ganin in da aka ƴantsar an sami cikakken zaman lafiya kamar yadda lamarin yake a wurin da ba a ƴantar ba?

BBC: To a matsayinka na ministan tsaro, yaushe 'yan Najeriya za su fara barci da duka idanunsu a rufe a yankuna kamar Dansadau a jihar Zamfara da Safana da Batsari a jihar Katsina?

Janar Magashi: To... ku bamu dan lokaci kadan. Gwamnatin tarayya na kokari irin wanda ya kamata. Suna bamu kayan aiki, kuma sun sa mu nemi masu aiki. Mun kuma tabbata idan aka ba 'yan sanda kayan aikin da suke bukata za su inganta ayyukan tsaro.

BBC: Zuwa yaushe?

Janar Magashi: In Allah ya yarda nan ba da dadewa ba za a yi...