Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar tsaro: 'Ya kamata a sauya salon yaƙi da 'yan ta'adda a Najeriya'
Kungiyoyin fafutukar kare hakkin bil'adama sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ceto 'yan kasar daga matsalolin rashin tsaro a kasar.
Kungiyoyi sama da goma ne su ka yi gangami domin nuna takaicin yadda matsalolin tsaro ke kara zama babbar matsala da har 'yan kasar suke neman saduda daga duk wani tsarin tsaro daga hukumomin kasar.
Sun bayyana haka ne ganin yadda ake ci gaba da fuskantar tarnaki da bijirewa daga 'yan ta'adda duk da kokarin da ake yi kan yaki da kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane.
Sun kuma koka kan yadda ake samun wasu daga al'ummar kasar da ke yi wa harkokin tsaro zagon kasa.
A cewar kungiyoyin, sai gwamnatin kasar ta sauya salon yadda ta ke tunkarar yaki da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane da gaskiya.
Wannan ne ya sa suka yi kira da a sauya salon jagorantar yaki sannan a samar da kayan yaki masu nagarta da zasu iya artabu da 'yan ta'adda da suka ce suna yi wa sojojin kasar barna ta rayuka wanda suke cewa hakan na zuwa sakamakon yadda wasu da ba su da masaniya kan harkokin tsaro ke cusa kansu a ciki.
Kwamared Funmi Jolade Ajayi na daga kungiyar samarwa mata mafita da sana'oi kuma ta shaida wa BBC cewa bayan an yaki cin hanci akwai kuma bukatar a inganta albashi da makaman yaki na zamani tare da sauraron matsalolin jami'an tsaro kai tsaye daga shugabanninsu.
'Sai an gyara hali za a ga sauyi'
Wasu dai na dorawa shugabannin soja da ke yaki da 'yan bindiga a kasar laifi da har suke kiran kawo gyaran fuska, to amma wasu daga cikin mahalarta taron kamar basarake Oba Hammed Adekunle Makama Owu na Kuta ya nuna abin da Najeriya ta ke bukata shi ne bayar da bayanan sirri kan tsaro.
Ya ce akwai bukatar 'yan kasa su nuna kishin kasarsu da sauya halayyarsu da gaske amma sauya shugabanni ba tare da sauya hali ba, ba zai samar da mafita ba.
"Rashin gama yakin nan ba laifin sojojin Najeriya ba ne, laifinmu 'yan Najeriya ne, idan mun ba Boko Haram (bayanai) mun hana sojoji ai mu muka ce a yi mutuwar wake kenan."
Mahalarta taron sun koka cewa suna mamaki yadda dakarun Najeriya suke galaba kan mayaka ko dawo da zaman lafiya ga wasu kasashe da aka gayyace su amma kuma rikici da matsalolin tsaro a cikin kasarsu ke gagararsu kawo karshensu.
Sun bukaci a cire harkokin siyasa da 'yan siyasa kan duk harkar da ta shafi tsaro a kasar.
Daraktan cibiyar kare dokokin kasa Kwamared Richard Akinola wanda ya halarci zaman ya ce dole a duba matsalolin tsaro da jami'an kafin a fara dorawa wasu laifi.
"Ana iya shaida duk wasu dabarun da ka ke da su, sannan ka yi amfani da su amma kuma karfin dakarunka na dawowa gidan jiya, ana karya lagon jami'an tsaro - to akwai bukatar shaida kawo wani sauyi. To amma sauya shugaba kadai ba zai haifar da samun nasarar yaki ba."
"Kalubalen da na ke hangowa na zuwa sakamakon zagon kasa da kuma yadda wasu ke tona asirin bayanan sirri na sojoji da rashin karawa sojojin kaimi sun taimaka wannan yaki ya dade. Saboda haka akwai bukatar manyan jami'an soja dasu sake fasalin yadda suke tunkarar yakin sunkuru da magabta."
Ana fama da karuwar matsalolin tsaro a baya-bayan nan a Najeriya kuma gwamnati a lokuta da dama ta sha ikirarin cewa tana ci gaba da kokari na ganin ta fitar da Najeriya daga kangin rashin tsaron.