Coronavirus a Najeriya: Me ya sa shugabanni ba sa ba da tazara?

Ga wasu daga cikin hotunan wasu daga cikin shugabannin a wuraren taruka mabanbanta ba tare da ba da tazara ba.

Duk da matakan da aka dauka na yaki da annobar korona a Najeriya na ba da tazara da wanke hannu da sanya takunkumi da hana taron mutane da yawa da dai sauransu.

Shugabannin da suke wannan kiraye-kiraye a mafi yawan hotunan tarukan da suke halarta ba su damu da su rika ba da tazara ba.

Ga wasu daga cikin hotunan wasu daga cikin shugabannin a wuraren taruka mabanbanta ba tare da ba da tazara ba.

A lokacin rantsar da shugabannin hukumar tabbatar da daidaito a ayyuka ta Najeriya.

A dai ranar ne aka rantsar da shugabannin hukumar ma'aikatan gwamnatin tarayya, da na hukumar da ke kula da harkokin kudi da ta tattara kudaden haraji na kasa.

Sai kaddamar da bututun mai da aka yi wanda zai taso daga Ajaokuta zuwa Kaduma har ya isa Kano.

Wanann hoton an dauke shi ne bayan wata tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki.

Hotunan da aka dauka bayan nada Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikwan kwaryar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Mun tuntubi wata majiya daga cikin makusantan gwamnatin jihar Kaduna kan wannan batu, sai dai ya ce wannan abu ba da gangan ba ne.

Sai dai mai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai, ya ce a wasu lokutan dakunan taron kanana ne ba za su ba da sukunin tabbatar da tazara ba tsakanin shugabanin.

Karin labarai masu alaka