Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Son, Mbappe, Zidane, Palmieri, da Jorginho

Adama Traore

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na son ɗaukar tauraron ɗan wasan Wolves, Adama Traore amma tana fuskantar barazana daga Man City da Liverpool da Barcelona da Juventus, a cewar jaridar Mail.

A gefe guda kuma, Wolves na son a biya ta fan miliyan 90 kan ɗan wasan mai shekara 24 ɗan ƙasar Spain.

TottenhamHotspur ta yi wa dan wasanta dan asalin Koriya ta Kudu Son Heung-min tayin sabuwar kwantiragi ta tsawon shekara biyar kan £200,000 a kowane mako ban da wasu alawus-alawus, matakin da ya kusan ninka albashinsa a kan kwantaraginsa mai ci da ake sa ran za ta kare a 2023. (Football Insider)

Kocin Spurs Jose Mourinho na sa ran Son mai shekara 28 zai sanya hannu kan sabuwar kwantaragin "nan ba da dadewa ba." (London Evening Standard)

Shirin Real Madrid na sake daukar dan wasan Paris St-Germain kuma dan Faransa Kylian Mbappe mai shekara 21 ba zai samu matsala ba ko da Zinedine Zidane ya bar kungiyar. (AS)

Zidane ya tabbatar cewa "yana tare da 'yan wasansa har mutuwa" bayan da ake ta hasashen cewa zai bar kungiyar ta Real. (ESPN)

Da alama ɗan wasan baya na Chelsea Emerson Palmieri mai shekara 26 zai bar Stamford Bridge a watan Janairu, kuma Inter Milan da Roma da kuma Napoli cikin kungiyoyi masu zawarcinsa. (Sky Sports Italia, via Express)

Manchester City na daf da daukan Filip Stevanovic, dan wasan Partizan kan fam miliyan 6 da zarar an bude damar sayen 'yan wasa a watan Janairu. Dan wasan mai shekara 18 dan asalin Serbia ya so tafiya Manchester United a baya. (Manchester Evening News)

Paris St-Germainna shirin kammala sabunta kwantaragin Neymar mai shekara 28 bayan amincewar baki da ya ba kungiyar. (Le10 Sport - in French)

Dan wasan Chelsea da Italiya Jorginho mai shekara 28 ya ce "a shirye yake" ya tattauna da Arsenal kuma ya ce akwai alamu masu karfi cewa GUnners na bukatar sa a wannan kakar wasan. (ESPN Brazil - in Portuguese)

Hukumar kwallon Kafa ta Ingila ta gargadi kungiyoyin kwallon kafa na kasar, inda ta ce za ta iya hana su dauko 'yan wasa daga Tarayyar Turai daga mako mai zuwa sai idan kungiyoyin da ke buga Gasar Firimiya sun amince su samar da dokokin da za su kare 'yan wasan kwallo 'yan asalin Birtaniya bayan ficewarta daga Tarayyar Turai. (Telegraph - subscription required)

Babu kanshin gaskiya cewa ɗan wasan kungiyar Burnley da Ingila James Tarkowski mai shekara 27 ya kusa sanya hannu a yarjejeniyar buga wa West Ham United, a cewa kocinta Sean Dyche. (Talksport)

Dan wasan Sfaniya Angelino mai shekara 23 ya ce ya damu da dalilin da ya sa bai buga wasanni masu yawa a Manchester City ba, amma ya kafe cewa ya sami karfin gwuiwa da ya koma RB Leipzig ta Jamus. (Marca, via Inside Futbol)