EndSARS: Muhimman wuraren da aka ƙona a zanga-zanga a Lagos

Zanga-zangar EndSARS da aka yi ta yi a wasu jihohin Najeriya ta janyo asarori da dama, kama daga kan lalata gine-ginen gwamnati da na ɓangarori masu zaman kansu a wasu jihohi musamman Legas.
Hukumomi sun baza jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin, sai dai tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa har a ranar Laraba.
Da daren jiya ne jami'an tsaro suka budawa wasu masu zanga zanga wuta a Lekki dake jihar Legas, abin da ya janyo jikkatar mutane masu yawa.
An bada rahotannin samun asaar rayuka da dukiyoyin jama'a, amma da yake gabatarwa al'ummar jihar jawabi, gwamnan Legas Sanwo Olu, ya ce ba wanda aka kashe, sanna ya ziyarci wadanda ke kwance a gadon asibiti don duba halin da suke ciki.
Ana ganin budewa masu zanga-zangar wuta ya taimaka wajen kazantuwar halin da ake ciki musamman a jihar ta Legas.
Ga wasu daga cikin muhimman guraren da aka bankawa wuta a ranar Larabar nan.
Hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA

Asalin hoton, AIT
Hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya dake Legas na cikin muhimman wuraren da ɓata gari suka kai wa hari.
Kamar sauran hukumomin gwamnati, akwai jami'an tsaro da aka jibge a hukumar da ke unguwar Marina, amma ba su iya daƙile al'amarin ba.
Babu wani cikakken bayani kan yadda aka cinna wuta ga hukumar ta NPA, amma wani bidiyo da kafar talabijin ta AIT a Najeriya ta wallafa a shafinta na Tuwitar ya nuna yadda ginin ke ƙonewa.
An ga motoci da wasu muhimman kayayyaki na ci da wuta a bidiyon da ke ta yawo a shafukan sada zumunta.
Gidan Oba na Legas

Rahotanni sun ce wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari gidan mai martaba Oba na Legas inda suka ɗauke sandan girmansa, kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito.
Sandar wata muhimmiyar alama ce ta mulki da ake bai wa masu riƙe da manyan sarautun gargajiya, don haka a matsayinsa na Sarkin Legas shi ma yana da ita.
Wasu majiyoyi sun ce 'yan dabar sun kunna kai gidan sarkin duk da tarin sojojin da aka jibge don gadinsa.
Hotunan da ke ta yawo a shafukan sada zumunta sun nuna maharan rike da sandar suna tafiya a fusace. Rahotanni sun ce sun so cinnawa gidan wuta ne baki daya, kafin daga bisani sojoji suka taka musu birki.
Mai martaba sarkin Oba na da daraja sosai ga al'ummar Legas, don haka kai hari gidansa ya bai wa jama'a da dama mamaki, kasancewarsa ba jami'in gwamnati ba.
Gidan talabijin na TVC

Asalin hoton, OTHERS
Wata ma'aikaciyar gidan talabijin ɗin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa suna cikin gabatar da shiri kai tsaye dole suka katse sakamakon 'yan daban da suka faɗo daƙin gabatar da shirye-shiryen nasu.
A halin yanzu dai gidan talabijin na TVC ɗin ya ɗauke, ma'ana ba a nuna tashar.
Wani bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ake ƙona wasu daga cikin motoci mallakar gidan talabijin ɗin.
Rahotanni na nuna cewa gidan talabijin ɗin mallakin tsohon gwamnan Legas ne Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa bai fito fili ya gasgata cewa shi ne ainahin mamallakin gidan talabijin ɗin ba.
Wasu mutane na ganin cewa yana da hannu a lamarin da ke faruwa, ko da yake ya fito ya musanta hakan.
Gidan mahaifiyar Gwamna Sanwo Olu

Asalin hoton, OTHERS
Gidan mahaifiyar gwamnan jihar Legas Sanwo Olu, na daga cikin wuraren da masu zanga-zangar suka cinna wa wuta kamar yadda kuke iya gani a wannan hoto da ke sama.
Gidan na unguwar Akelere da ke Sulurele, sai dai babu tabbacin ko mahaifiyar gwamnan na ciki lokacin da al'amarin ya faru.
An ga yadda wuta ke ci ganga-ganga a gidan, bayan da 'yan dabar suka banka ta.
Tashar mota ta Oyingbo

Asalin hoton, OTHERS
Ita ma tashar mota ta Oyingbo da ke cikin birnin Legas ba ta tsira ba, domin kuwa an cinna wa motocin haya da dama wuta.
Jariridu a Najeriya sun rawaito cewa an ƙona akalla motocin safa 20, sakamakon wannan al'amari.
An ga mutane na fitowa daga tashar motar suna gudu domin tsira da ransu, yayin da su kuma maharan ke rarakarsu a guje.
Otel din Orientel

Asalin hoton, OTHERS
Kamar gidan talabijin na TVC, shi ma katafaren otel din Oriental da ya yi shuhura wajen karbar baƙi a jihar Legas, mallakin tsohon gwamnan Legas ne Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun banka wa otel din Oriental wuta tun daren ranar Talata, jim kadan bayan buɗewa masu zanga-zangar wuta, abin da ya janyo ƙona bangarori da dama.
Wasu rahoanni sun ce sun watsawa otel din da ke unguwar Lekki - Epe Expy da Victoria Island fetur, kafin daga bisani su cinna masa wuta.
Ofisoshin ƴan sanda

Asalin hoton, OTHERS
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Najeriya sun ce aƙalla ofisoshin ƴan sanda 12 aka kai wa hari, an kona da dama da kuma tafka ta'adi. Daga cikin inda aka kona akwai ofishin ƴan sanda da ke Iganmu.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Legas ya tabbatar da cewa 'yan daba sun cinna wuta a ofishinsu da ke Iganmu.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata, sannan lamarin ya janyo jikkatar wasu jami'anta, da mutuwar wani guda.
Rundunar ta ce tana da masaniyar cewa wasu ɓata gari da ke neman fakewa da zanga-zangar EndSARS na haifar da yamutsi a jihar, don haka ta gargadi iyaye su ja kunnen 'ya'yansu.
Ta lashi takobin yin dukkanin mai yiwuwa don tabbatuwar zaman lafiya a jihar, da manufar kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Babbar Kotun da ke Igbosere
A ranar Laraba wasu da ake zargin ɓata gari ne sun shiga Babbar Kotun da ke Igbosere a Lagos a ranar Laraba inda suk sace kumfutoci da iya kwandishan da sauran kayayyaki.
Wani bidiyo da ya yadu kamar wutar daji ya nuna yadda wasu daga cikin su suka sanya rigar da alƙali ke sawa, ɗauke da adduna a hannunsu.
Bayan da suka sace iya abubuwan da suke so sai suka cinna wa kotun wuta suka gudu.
Ofishin hukumar Road Safety da VIO Ojodu
A ranar Larabar ne dai kuma ɓata garin suka kai hari ofisoshin hukumar kare afkuwar haɗurra ta ƙasa FRSC da kuma hukumar da ke binciken ababen hawa VIO a Ojodu da ke Legas inda suka cinna wuta.
Shaidu sun ce an ƙona motoci da dama a wajen.











