EndSars: Buhari ya buƙaci 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan kasar su kwantar da hankalinsu bayan zanga-zangar EndSARS ta rikide zuwa tarzoma a wasu sassan kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a sanarwar da kakakinsa Femi Adesina ya aike wa manema labarai ranar Laraba.
"Fadar shugaban kasa tana rokon a fahimce ta sannan a kwantar da hankali a duka fadin kasa, a yayin da shirin kawo sauyi kan harkokin 'yan sanda ke ci gaba da wakana a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi", in ji sanarwar.
Ya yaba wa jihohin da suka kaddamar da kwamitocin yin garanbawul ga rundunar 'yan sanda, yana mai cewa hakan ya nuna cewa a shirye suke su aiwatar da sauye-sauyen."A lissafinmu na karshe, jihohin da ba su gaza 13 ba sun kaddamar da kwamitocin shari'a domin samar da mafita da kuma yin adalci ga mutanen da 'yan sanda suka musgunawa kamar yadda Majalisar Tattalin Arziki ta nemi su yi," a cewar Shugaba Buhari.
Kawo yanzu jihohin da suka kafa kwamitocin sun ƙunshi Lagos, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Enugu, Imo, Plateau, Edo, Nasarawa, Ondo da kuma Akwa Ibom.Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa ta dade tana fafutukar ganin an kawo sauyi kan ayyukan 'yan sandan Najeriya, ciki har da matakan da suka dauka na kafa kwamitin shari'a da zai tattabar da adalci kan mutanen da 'yan sanda suka ci zarafi a jihohi da kuma sanya hannu kan kudurin dokar samar da gidauniyar 'yan sanda.
Kazalika a shekarar 2018, Shugaba Buhari ya amince a kara albashin 'yan sanda inda aka kara kasafin kudinsu na shekara-shekara daga naira biliyan 288 a 2018 zuwa naira biliyan 417 a kasafin kudin 2021; karin kashi 45 cikin dari, in ji sanarwar.

Asalin hoton, EPA
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ake zargi sojojn Najeriya sun bude wuta kan dubban masu zanga-zangar EndSARS a birnin Lagos ranar Talata da almuru lamarin da rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwa akalla 12 da jikkatar mutane da dama.
Kazalika kiran nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jihohin da dama suka sanya dokar hana fita da zummar takaita bazuwar zanga-zangar wadda aka soma mako uku da suka gabata.











