Ƴan sandan Faransa sun kai samame gidajen 'masu kaifin kishin Musulunci'

Asalin hoton, EPA
'Yan sandan Faransa sun kai samame gidajen wasu gomman mutane da ake zargin masu kaifin kishin Islama ne, biyo bayan sare kan malamin makarantar nan da ya nuna wa ɗalibansa hoton barkwanci da ke nuna fiyayyen halitta.
Wasu daga cikin waɗanda aka kai wa samamen sun wallafa saƙonnin nunawa maharin da ya sare kan malamin goyon baya.
Sannan gwamnati ta ce za ta gurfanar da wasu ƙungiyoyin Musulmi 51 na ƙasar a kotu.
'Yan sandan sun harbe makashin Samuel Party a ranar Juma'a.
Makarantar da malamin ke koyarwa na Conflans-Sainte-Honorine ne, wani yanki da ke can bayan gari a yammacin birnin Paris.
Maharin mai shekara 18 wanda ɗan yankin Ceceniya ne ba shi da wata alaƙa da malamin a makaranta.
A ranar Litinin Ministan Harkokin Cikin Gida na Fransa Gérald Darmanin, ya ce samamen ya aika ƙwaƙƙwaran saƙon cewa maƙiyan Faransa ba su da damar sakewa, sannan za a ci gaba da kai shi a ko wanne mako.
Ya ce ba wai dukkanin mutanen da aka kai wa samamen ne ke da hannu a kisan Mista Party ba.
A gefe guda kuma 'yan sanda za su binciki wasu mutum 80 da suka wallafa saƙonnin nuna goyon bayansu ga maharin da ya aikawa wannan al'amari.
Gwamnati ta ce matsawar aka samu ƙungiyoyin Musulmi da yaɗa maganganun tsanar wasu, to kuwa za a rushe su nan take.
Cikin kungiyoyin har da wata mai fafutukar hana ƙyamar Musulmai, wadda gwamnati ke kallon tana yaɗa manufar ƙyamar ƙasa a tsakanin al'ummar Musulmi mazauna Faransa.
A wannan shafin, ƙungiyar ta kira kanta a matsayin ta kare hakkin 'yan adam, kuma babban aikinta shi ne yaƙi da ƙyamar Musulunci, kuma tana aiki ne da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asalin hoton, AFP

Menene sakamakon bincike na baya-bayan nan?
Mai gabatar da ƙara kan ta'addancin Jean-François Ricard, ya ce mamacin wato Mista Party ya riƙa samun saƙonnin barazana tun lokacin da ya nuna hoton barkwancin da ke nuna Annabi SAW, a matsayin ƴancin faɗin albarkacin baki.
Kamar yadda ya sha yi a shekarun baya-bayan nan, Mista Party wanda malamin tarihi ne, ya kan buƙaci ɗalibai Musulmai su riƙa kai zuciya nesa a duk sanda suka ga kamar an yi musu ɓatanci.
Ɓatanci ga Annabi SAW na iya haifar da ɓacin rai ga Musulmai, sannan a addinance ma babu kyau a zana hoton Annabi ko kuma Allah Mahalicci.
Wannan batu ne mai haɗari a Faransa, musamman sakamakon yaɗa hotunan barkwanci na Manzon Allah SAW da jaridar nan ta Charlie Hebdo ta yi a shekarun baya-bayan nan.
Sannan har yanzu ana ci gaba da shari'a dangane da kisan wasu mutum 12 a wajen ofishin jaridar a shekarar 2015.
Wasu Musulmai a Faransa na cewa suna fama da haɗarin cin zarafi da ɓatanci, saboda abin da suka yi imani da shi, batun da ya sha haifar da ce-ce ku-ce a ƙasar.
An kama wasu mutum 11 dangane da kisan Mista Party, a wani ɓangare na binciken da 'yan sanda ke yi, daga haka babu wani ƙarin bayani.

Asalin hoton, Getty Images
Menene martanin da mutane ke yi a Faransa?
Harin ya ruɗa Faransa, dubban mutane sun taru a gangamin da aka gudanar a ƙarshen mako don yin jimamin mutuwarsa.
Wani mutumi daga cikin masu gangamin na dauke da wata alama da ke cewa "Babu wata dama ga maƙiya ƙasarmu''
Wani kuwa na riƙe da wata alama da ke cewa "Ni farfesa ne. Ina tuna ka, Samuel''
"Shugabannin usulmai a Faransa sun la'anci harin.
Tareq Oubrou, limamin wani masallaci a Bordeaux, ya ce suna tir da wannan hari.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce da alama harin na da alaƙa da harin ta'addancin masu ikirarin jihadi.
An ruwaito shi yana cewa ''ba za mu bar su su zauna lafiya ba''.

Asalin hoton, Reuters
Bayan gangamin ranar Lahadi, an kuma shirya taron ta'aziyya ga Samuel Party ranar Laraba.
Me ya faru ranar Juma'a?
Mista Ricard ya ce maharin wanda ke zaune a wani gari mai nisan kilomita 100 daga inda ya yi kisan ya je makarantar da malamin ke koyarwa a ranar Juma'a, har ma ya buƙaci ɗalibansa su nuna masa malamin.
Ba shi da wata alaƙa da malamin ko ma makarantar da yake koyarwa.
Ya bi sahun malamin bayan ya tashi daga aiki, inda ya yi amfani da wuƙa wajen daɓa masa a kansa, sannan ya fille masa kai daga bisani.
Shaidu sun ce an ji maharin na ihu yayin da yake sare kan malamin.
Yayin da 'yan sanda suka kusance shi, ya harbe su da bindiga, daga nan ne suma suka mayar masa da martani tare da samunsa sau tara.
An ga wata ƴar gajeruwar wuƙa a kusa da shi.
Mahunkunta sun ce mutum ya sha gurfana a kotu, amma saboda ƙananan laifuka.











