Charlie Hebdo: An soma shari'ar mutanen da suka hari ofishin mujallar da ta yi ɓatanci ga Manzon Allah

Mujallar Charlie Hebdo

Asalin hoton, Getty Images

An soma shari'ar mutum 14 a Faransa bisa kai mummunan hari a kan mujallar nan ta kasar Faransar Charlie Hebdo wadda ta shahara wurin zanen barkwanci fiye da shekaru biyar da suka gabata.

Galibinsu sun gurfana a gaban kotun da ke birnin Paris a ranar Laraba, amma uku daga cikinsu ana yi musu shari'ar ne ba tare da suna kotun ba.

Ana zarginsu ne da taimaka wa masu tayar da kayar baya wadanda suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 12 a ciki da kewayen ofishin mujallar a watan Janairun 2015.

Daya daga cikinsu kuwa harbin wata 'yar sanda ya yi mace tare da kai hari kan wani katafaren shago.

An kashe akalla mutum 17 a cikin kwanaki uku.

Wadannan kashe-kashen su ne kashin bayan hare-haren masu jihadi a cikin Faransa abin da ya janyo mutuwar mutum 250.

Mujallar ta sake wallafa wani zane na barkwanci inda suka siffanta Annabi Muhammad S.A.W.

Sake wallafa zanen na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari'ar mutanen nan 14 da ake zargi da taimaka wa wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi da kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.

An kashe mutum 12, ciki har da wasu shahararrun masu zanen barkwanci. An sake kashe wasu mutum biyar a wani hari na daban a birnin Paris kwanaki biyar bayan harin farkon.

Waɗannan hare-haren su ne mafarar kai hare-haren masu ikirarin jihadi a fadin Faransa.

Shafin farko na mujallar na ɗauke da zanen barkwanci har guda 12 na Annabi Muhammad S.A.W, waɗanda aka wallafa a wata jaridar harshen Danish kafin aka wallafa su a mujallar Charlie Hebdo.

Ɗaya daga cikin zanen barkwancin ya nuna Annabi Muhammad S.A.W sanye da bam a kansa a maimakon rawani.

A sharhin da ta wallafa, mujallar ta ce tun abin da ya faru a 2015 ake yin kira a gare ta da ta ci gaba da zane-zanen barkwanci.

"A kullum mun ƙi yin hakan, ba wai don za a hana ba - doka ta ba mu damar mu yi hakan - amma muna buƙatar hujja mai kwari don mu yi hakan, hujja wadda ke da ma'ana kuma wadda za ta kawo wani abu na muhawara," in ji mujallar.

Ta kara da cewa: "Sake wallafa irin wannan zanen a makon da ake yin shari'ar waɗanda suka kai hare-haren 2015 abu ne mai muhimmanci a gare mu."

Wannan layi ne

Mene ne yake faruwa a kotun?

trial

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana gudanar da shari'ar ne cikin tsattsauran matakin tsaro

Mutum 11 da ke kare kansu sun gurfana a kotun ranar Laraba. Sun bayyana sunaye da kuma sana'o'insu, kuma dukkansu sun tabbatar da cewa a shirye suke su bai wa kotu amsa.

An so a fara shari'ar ne tun a watan Maris, amma aka ɗage sakamakon annobar korona.

Ana sa ran za a kammala shari'ar a watan Nuwambar shekarar nan.

Ana zargin mutum 14 da samun makamai da kuma bayar da taimako ga waɗanda suka kai hari a ofishin Mujallar Charlie Hebdo da ke birnin Paris, da kuma taimakawa wajen kai wasu hare-hare a wani babban kantin Yahudawa da kuma wani ɗan sanda.

Mutum uku daga cikin waɗanda ake zargi ana shari'arsu ne ba tare da suna nan ba sakamakon zargin da ake yi cewa sun gudu zuwa arewacin Syria da Iraƙi.

Ana tunanin akwai kusan mutum 200 da suka shigar da ƙara gaban kotu kan lamarin kuma ana sa ran waɗanda suka tsallake rijiya da baya yayin harin za su bayar da shaida a gaban kotun, kamar yadda mai bayar da rahoto a kafar watsa labarai ta RFI ya bayyana.

Wannan layi ne

Me ya faru a 2015?

A ranar 7 ga watan Janairu, wasu 'yan gida ɗaya, Said da Cherif Kouachi suka afka ofishin Charlie Hebdo, inda suka buɗe wuta suka kashe editan mujallar Stéphane Charbonnier, wanda aka fi sani da Charb, tare da wasu mutum huɗu masu zanen barkwanci da wani baƙo da ya je halartar wata tattaunawa da kuma wani mai kula da wurin. An kuma harbe dogarin editan mujallar da wani ɗan sanda.

A daidai lokacin da 'yan sanda ke neman 'yan uwan biyu da suka kai harin - waɗanda daga baya aka kashe - sai kuma aka kai wani harin a gabashin Paris. Amedy Coulibaly wanda abokin Said da Cherif ne ya kashe wata 'yar sanda, inda ya yi garkuwa da mutum da dama a wani babban kantin Yahudawa.

Ya kashe wasu Yahudawa huɗu a ranar 9 ga watan Janairu kafin aka kashe shi yayin wata arangama da ya yi da 'yan sanda.

A wani bidiyo da aka naɗa, Coulibaly ya bayyana cewa an kai hare-haren ne da sunan ƙungiyar IS.

Karin labarai da za ku so ku karanta: