Omar al Bashir: Gwamnatin Sudan za ta miƙa Omar al Bashir ga kotun ICC

Wata tawaga daga kotun kasa da kasa mai hukunta masu aikata manyan laifuka ta isa Sudan domin tattauna batun shari'ar Shugaba Omar al-Bashir.

Kotun ta ICC na neman a mika ma ta al-Bashir domin ta hukunta shi kan tuhumar da ake ma sa da aikata laifukan kisan kiyashi da ya yi wa al'umomin kasar da laifukan yaki da kuma take hakkin bil Adama.

Firaministan Sudan mai ci ya ce tawagar za ta kai ranar 21 ga Oktoba a kasar domin tattauna abin da ya kira "haɗin kai kan batun shari'ar".

Gwamnatin Sudan ta amince a gurfanar da shi a kotun kasa da kasa da ke birnin Hague.

Amma gwamnatin ta kuma amince da kafa wata kotu ta musamman da za ta yi wa wadanda suka aikata laifukan yaki shari'a karkashin wata yarjejeniya da ta kulla da 'yan tawayen kasar.

Cikin manyan jami'an kotun da suka isa Sudan akwai Fatou Bensouda.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kiyasta kimanin mutum 300,000 aka kashe a yakin da aka yi wanda ya samo asalai daga wani bore a Darfur a 2003.

Kotun na tuhumar wasu tsofaffin jami'an gwamnatin biyu, Ahmed Haroun da Abdelrahim Mohamed Hussein da aikata laifukan yaki da take hakkin bil Adama da ata ce sun aikata a yankin.

An hambare Omar al-Bashir mai shekara 76 daga mulki ne bayan da dubun-dubatan al'umar kasar suka yi ma sa bore.

A halin yanzu wata gwamnatin rikon kwarya ce ke mulkin kasar wadda ta hada da sojoji da fararen hula.

Tuni wata kotu ta sami tsohon shugaban da laifin cin hanci. Shi da wasu mutum 27 na fuskantar shari'a a Khartoum kan tuhume-tuhumen da suka danganci juyin mulkin da ya jagoranta a 1989.

Idan aka same su da laifin, suna iya fuskantar hukuncin kisa.

Tsohon shugaban ya musanta tuhume-tuhumen, kuma wani lauyansa ya ce al-Bashir da sauran wadanda ake tuhuma na fuskantar shari'ar ne saboda dalilai na siyasa, kua ana tsare da su a yanayin da yake na muzgunawa.