Abin da ya sa Trump yake so Sudan ta yi ƙawance da Isra'ila

    • Marubuci, Daga Alex De Waal
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Masanin Sudan

A yayin da Sudan ke cikin mawuyacin hali - tabarbarewar tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin abinci a fadin kasar - gwamnatin Amurka ta Shugaba Donald Trump da gwamnatin Isra'ila sun samu wata dama.

Fatan al'ummar kasar ya dogara ne da zanga-zangar watanni 18 da aka yi da ta kai ga kawo karshen mulkin shugaban da ya fi dadewa a kan mulkin kasar Omar al-Bashir

Amma idan Sudan ta yarda da Isra'ila, Amurka za ta cire ta daga cikin jerin kasashen da ke tallafa wa 'yan ta'adda, tare da bude kofar saita tattalin arzikin kasar.

Labarin na da sarkakiya wanda ya samo asali shekaru 30 baya tun farkon kafuwar gwamnatin musuluncin kasar.

Bayan kwace mulki ta hanyar juyin mulki a 1989, Shugaba al-Bashir ya mayar da Khartoum cibiyar masu da'awar jihadi ta duniya.

Al Qaeda da sauran kungiyoyi irinta sun mayar da Sudan wani sansani na kaddamar da hare-hare kan Amurka da Saudiyya da Masar da Habasha da Uganda da Kenya da sauran wurare.

Bayan harin farko da aka kai cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya a New York a 1993, Amurka ta saka sunan Sudan cikin jerin kasashe da ke daukar nauyin ta'addanci.

Hadin gwiwar CIA

Takunkumin kasashen duniya na kudi da matsin lambar soji daga kasashe makwabta da suke goyon bayan 'yan tawayen Sudan ya tursasa wa Sudan korar Osama bin Laden da wasu mayakan jihadi daga kasar.

Bayan harin 11 ga Satumban 2001, jami'an leken asirin Sudan suka zama abokan huldar hukumar leken asirin Amurka ta (CIA).

Kan wannan, ya kamata a cire Sudan daga cikin jerin kasashen da ke taimakawa ta'addanci.

Amma mambobin majalisar sun nuna kiyayya ga Khartoum saboda wasu dalilai masu yawa, ciki har da yakin Darfur da take hakkin dan adam, kuma jerin sunayen ya ci gaba.

Amma gwamnatin al-Bashir ta ci gaba da aikinta a sirance, inda ta ci gaba da alakarta da Iran da Hamas, kuma akalla sau biyu jiragen yakin Isra'ila sun kai wa wata tawaga hari da ke tafiya a ruwan Sudan, da ake zargin makamai ne za a kai wa Hamas

A 2016, saboda matsin lamba daga Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, gwamnatin Bashir ta katse huldarta da Iran.

Amma duk da juyin juya halin da aka yi a bara, Amurka ta ki sauyawa.

Jami'an harkokin wajen Amurka suna son su yi tanadin babbar damar da suke da ita, domin suna tunanin sabuwar gwamnatin ba za ta dore ba.

Ƴan majalisar dattawa sun hana cire sunan Sudan

Matsalar ita ce ci gaba da sanya takunkumin a Sudan na iya zama wani abin da ƙasar ke tunani na la'antarta ga gazawa.

Idan har Sudan ta ci gaba da zama cikin jerin sunayen, takunkuman suka ci gaba da gurgunta kasuwancin kasar, zuba hannayen jarin kasashe ya tabu kuma asusun lamuni na duniya da Bankin Duniya ba za su iya samar da hurumin tallafa wa kasar ba daga dimbin bashin da ake bin ta - $72bn wanda ke ci gaba da karuwa.

Wannan kuma ya kara tsananta saboda kullen annobar korona da kuma ambaliyar ruwa.

A watannin baya, yarjejeniyar cire kasar daga jerin sunayen 'yan ta'adda a hankali ya samu shiga majalisar dattijan Amurka, daga bukatu na ƴan uwan wadanda hare-haren al Qaeda suka kashe a gabashin Afirka da Yemen cewa sai an biya diyya.

Sudan ta amince ta biya dala miliyan 335. Amma a Satumba sanatocin jam'iyyar Demokurat - Chuck Schumer da Bob Menende sun toshe damar.

Gwamnatin Trump yanzu ta yi wa Sudan tayin mafita.

Ziyarar da ya kai Khartoum a karshen Agusta, Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya gabatar da wata bukata ga Firaministan Sudan Abdalla Hamdok: Idan har Sudan ta amince da Isra'ila, Shugaba Trump zai keta tarnakin da aka samu a majalisa.

Bayan matakin da Daular Larabawa ta dauka a watan da ya gabata, Sudan mamba a kungiyar kasashen Larabawa, za ta kasance kasar Larabawa ta biyar da za ra dauki irin matakin.

Zai kasance babban ci gaba ga alkawalin gwamnatin Trump na farfado da hulda tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila cikin makwanni kafin zabe.

Amincewa da Isra'ila babban mataki ne ga Sudan - ita ce babbar manufar.

Karfin ikon manyan hafsoshin soji

Mista Hamdok ya san cewa kawancensa da gamayyar kungiyoyin fararen hula zai iya wargajewa idan har ya dauki matakin.

Ya shaida wa Mista Pompeo cewa ya kamata matakin ya jira har a zabi sabuwar gwamnati a shekaru uku masu zuwa.

Duk da cewa Mista Hamdok da majalisar ministocinsa na kan mulki, manyan hafososhin sojin Sudan ne ke da karfin iko.

Wanda ya samu goyon bayan Daular Larabawa da Saudiya da Masar, shugaban gwamnatin rikon kwaryar Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Janar Mohamed Hamdan Dagolo, wanda aka fi sani da "Hemeti", su ke ba sojoji iko da kuma kula da harakokin kudi.

Kuma wadannan hafsoshin sojin ne ke magana da Isra'ila kai-tsaye. Jansr Burhan ya gana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Fabrairu - ba tare da sanar da Hamdok ba - kuma za su sake haduwa nan gaba.

Ga Janar Burhan da Janar Hemeti, yarjejeniyar Amurka kan Isra'ila ta yi masu alkawalin amincewar kasashen duniya idan ba su kawo cikas ba ga dimokuradiyyar kasar.

Wannan ya sa 'yan siyasar Sudan suka bukaci a yi nazari sosai kan yarjejeniyar

Lokacin da zanga-zangar da ta yi awon gaba da Bash ir a watan Afrilun bara, Janar Burhan da Janar Hamdok suka haye kan mulki, bayan wata biyu sojojinsu suka kashe masu zanga-zanga sama da da 100

Wannan ya haifar da bore, inda yarjejeniyar da Amurka da Birtaniya da Saudiyya da Daular Larabawa suka amince a raba madafan iko da fararen hula.

Babban batu shi ne cewa sojoji sun yi hakuri ne da fararen hula kawai saboda suna son samun girmamawa daga kasashen duniya. Amma al'ummar Sudan ba su yafe wa sojojin ba kan kashe mutanen da suka yi.

Tsoffin mutanen Sudan suna tuna yarjejeniyar da ake kira Operation Moses,da aka yi a asirce a 1984 tsakanin tsohon shugaban kasar Jaafar Nimeiri wacce a lokacin ta bai wa Isra'ila damar jigilar yahudawan Habasha daga sansanin 'yan gudun hijira a Sudan. Daga baya an zargi Nimeiri da almundahanar kudi ta miliyoyin daloli daga Mossad, hukumar leken asirin Isra'ila.

Alex de Waal shi ne babban daraktan cibiyar tabbatar da zaman lafiya ta duniya a sashen nazarin shari'a da diflomasiya a jami'ar Tufts University da ke Amurka.