Salihu Tanko Yakasai: Ganduje ya dakatar da mai ba shi shawara saboda sukar Buhari

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mataimakinsa na musamman kan kafafen yaɗa labarai, Salihu Tanko Yakasai kan wata suka da Salihun ya yi a shafin Twitter ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Lahadi, ya ce umarnin na gwamnan zai fara aiki ne nan take.

A safiyar yau ne dai Malam Salihu Tanko Yakasai, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter inda ya danganta Shugaban Najeriyar da "mara tausayi", sai dai sa'o'i kaɗan ya goge wani ɓangare na saƙon da ya wallafa.

Salihu Yakasai na mayar da martani ne game da jan ƙafar da Buhari ya yi game da kiraye-kirayen da 'yan Najeriya ke yi na rushe rundunar SARS ta 'yan sanda sakamakon zargin cin zarafi da azabtarwa da ake zarginsu da yi.

"Ban taɓa ganin gwamnatin da ba ta tausayin al'ummarta ba kamar ta Muhammadu Buhari," in ji Salihu Yakasai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ci gaba da cewa: "A lokuta da dama ya gaza lallaɓa al'ummarsa [Buhari] da kwantar musu da hankali yayin da suke cikin tashin hankali.

"Ba za ka iya yi wa al'ummarka jawabi ba na minti biyar, waɗanda ka bi jihohi 36 kana barar ƙuri'unsu, ya zama kamar wata alfarma kake yi musu."

Duk da cewa Buhari ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar Mohammed Adamu a daren Juma'a tare da bayar da umarnin ɗaukar mataki, Salihu yana ganin ya kamata a ce Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi da bakinsa.

Sai dai sa'o'i kaɗan kafin dakatar da Salihu, Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya ya sanar da rushe rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS a ƙasar bayan an shafe kwanaki ana jerin zanga-zanga a tituna da kuma kafofin sada zumunta.