Man Utd da Man City na son Pochettino

Manchester United da Manchester City suna duba yiwuwar daukar tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino , a cewar Sunday Mirror

Babban jami'an Manchester United Ed Woodward ba zai yi wata-wata ba wurin sallamar kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer idan suka ci gaba da shan kashi a kwallon kafa. (Sunday Mirror)

West Ham ta mika £17m tare da karin alawus domin dauko dan wasan Brentford dan kasar Algeria Said Benrahma, mai shekara 25. (90 Min)

Dan wasan Tottenham Gareth Bale zai iya taka muhimmiyar rawa wajen dauko dan yankinsu na kuma dan wasan Swansea Joe Rodon, mai shekara 22, a makon nan. (Star on Sunday)

Leicester tana son dauko Rodon amma ta fi so ta yi zawarcinsa a watan Janairu ko kuma bazara mai zuwa. (Star on Sunday)

Golan Stoke dan kasar Ingila Jack Butland, mai shekara 27, zai iya bayar da mamaki inda zai tafi Liverpool. (Sunday Mirror)

Dan wasan Belgium Romelu Lukaku ya gargadi dan wasan gaban Chile Alexis Sanchez da Ashley Young da su bar Manchester United sannan su bi shi Inter Milan saboda 'rabuwar kawunan' da ake samu a Old Trafford. (La Repubblica, via Mail on Sunday)

Dan wasan da Chelsea ta saya kwanan baya Kai Havertz, dan kasar Jamus mai shekara 21, ya ce dimin da ke cikin gasar Firimiya yana da "gajiyarwa" idan aka kwatanta da ledar da yake murzawa a Bundesliga. (Evening Standard)

Dan kasar Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, ya ce tattaunawar da ya yi da Ole Gunnar Solskjaer ce ta ja hankalinsa ya tafi Manchester United. (ESPN)

Dan wasan Manchester City dan kasar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 29, ya ce akwai kwararrun 'yan wasa a kungiyar ko da a ce ta gaza dauko dan wasan Barcelona Lionel Messi, mai shekara 33, a bazara yana mai dagewa cewa, "Ni ban damu da zuwansa ba ". (Manchester Evening News)

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya dage cewa Mesut Ozil, mai shekara 31, zai iya ci gaba da taka muhimmiyar rawa a Gunners. (Goal)