Za a kama wasu 'yan majalisar Kenya saboda hayar 'yan bangar siyasa

Mutanen biyu sun jima da batawa saboda kokarin mataimakin shugaban kasar na tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutanen biyu sun jima da batawa saboda kokarin mataimakin shugaban kasar na tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Shugaban rundunar 'yan sandan Kenya ya ba da umarnin kama wasu 'yan majalisar dokoki biyu dangane da barkewar rikici tsakanin magoya bayan wasu 'yan siyasa na bangaren 'yan hamayya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Ana zargin Ndindi Nyoro da Alice Wahome da hayar mutane don tayar da rikici a Yankin Muranga da ke tsakiyar Kenya, tsakanin magoya bayan shugaba Uhuru Kenyatta da wadanda ke mara wa mataimakinsa, William Ruto baya.

Lamarin ya faru ne yayin da Mista William Ruto ya halarci hidimar coci a yankin da shugaban kasar ke da karfi.

Masu aiko da rahotanni sun ce tashin hankalin alama ce ta damuwa gabanin zabukan kasar na gaba wanda ake ganin Mista Ruto na da niyyar tsayawa takarar shugabancin kasar.

Shugaban kasar da mataimakinsa sun jima da batawa, kuma ana danganta hakan da kokarin mataimakin shugaban na tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Masu sharhi na ganin rikicin da aka fara samu tun yanzu yayin da ya rage saura kusan shekaru biyu a gudanar da zabe ya nuna abin da ka iya faruwa idan lokacin zaben ya zo.

A zaben da ya gabata ma dai an tafka rikici a kasar, bayan da hukumar zabe ta ayyana shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya samu nasara.

Tun kafin a kai ga sanar da sakamako a hukumance ne dan takarar jam'iyyar adawa Raila Odinga ya sanar da kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, abin da ya janyo magoya bayansa suka kwarara a kan tituna bayan sanar da abin da ya sabawa ra'ayinsu.

Lamarin ya janyo gagarumin tashin hankali, kafin daga bisani 'yan siyasar biyu suka sasanta da juna tare da kwantar da hankulan magoya bayansu.