Donald Trump, Amitabh Bachchan, Paul Pogba: Wasu daga cikin mashahuran mutanen da suka kamu da coronavirus a duniya

Donald Trump, Amitabh Bachchan, Paul Pogba:
Bayanan hoto, COVID-19 ta kama mutum fiye da miliyan 34 a duniya
Lokacin karatu: Minti 4

Cutar korona ta mamaye aƙalla ƙasashe da yankuna 188, inda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum miliyan daya kawo yanzu.

Alƙaluman da Jami'ar Johns Hopkins ta fitar ranar Juma'a sun nuna cewa cutar ta kama mutum fiye da miliyan 34 a faɗin duniya kuma tana ci gaba da mamaye sassa daban-daban, yayin da a wasu ƙasashen take sake yaɗuwa a zagaye na biyu.

Mun yi nazari kan wasu daga cikin shahararrun mutane da cutar ta kama a duniya, daga shugabannin ƙasashe, zuwa manyan jami'an gwamnati, daga mawaƙa da taurarin fina-finai zuwa 'yan ƙwallo.

Shahararrun mutanen da cutar ta kama sun haɗa da Yarima Charles, tauraron fina-finan India Amitabh Bachchan, Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya.

Donald Trump da Melania Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi da matarsa Melania sun kamu da cutar korona.

Ya sanar da haka ne a shafinsa na Tiwita ranar Alhamis da tsakar dare a agogon Amurka.

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya sanar da cewa wata babbar hadimarsa Hope Hicks ta kamu da cutar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Likitan Mr Trump Sean Conley ya fitar a sanarwa, yana mai cewa shugaban kasa da mai dakinsa "suna cikin koshin lafiya a wannan lokaci, kuma sun ce za su ci gaba da zama a gidansu na White House domin yin jinya".

"Ina mai tabbatar muku cewa shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba a yayin da yake murmurewa, kuma zan rika sanar da ku halin da suke ciki nan gaba," in ji sanarwar.

Boris Johnson: Ranar 27 ga watan Maris ne Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson, mai shekara 55, ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona.

An kwantar da Mista Johnson asibiti ranar 5 ga watan Afrilu bayan sanarwar fadar Downing Street ta ce "Sakamakon gwajinsa ya nuna yana dauke da cutar, kuma ya yi gwajin ne bisa shawarar da babban likitan gwamnatin kasar Farfesa Chris Whitty ya ba shi.''

Ranar 6 ga watan Afrilu an garzaya da Mista Johnson sashen bayar da kulawar gaggawa sakamakon tabarbarewar da yanayinsa ya yi, sannan ya bukaci Sakataren Wajen Birtaniya Dominic Raab ya rika gudanar da ayyukan kasar "kamar yadda ya kamata."

Jair Bolsonaro: Shugaban Brazil ya kamu da cutar COVID-19 ranar 7 ga watan Yulin da ya wuce bayan ya dade yana cewa cutar ba gaskiya ba ce.

Michelle Bolsonaro: Mai dakin shugaban Brazil ta kamu da cutar korona, a cewar sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ranar 30 ga watan Yuli, kwana biyar bayan mai gidanta, Jair Bolsonaro ya warke daga cutar.

Abba Kyari - A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari, ya kamu da cutar korona bayan komawarsa kasar daga Jamus. Cutar ta yi ajalinsa ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.

Yarima Charles: Yariman Wales kuma daya daga cikin masu jiran gadon sarautar Birtaniya ya kamu da cutar koronar a ranar 25 ga watan Maris. Yariman mai shekara 71 ya nuna alamar cutar kadan a lokaci -"amma yana cikin koshin lafiya",a cewar mai magana da yawun gidan sarautar Birtaniya.

Kazalika an yi wa matar Charles, Camilla, gwajin cutar amma ya nuna cewa ba ta dauke da ita.

Silvio Berlusconi: Tsohon Firai Ministan Italiya ya kamu da cutar korona ranar 2 ga watan Satumba tare da 'ya'yansa biyu.

Wannan layi ne
..

Asalin hoton, Getty Images

Amitabh Bachchan da iyalansa: Shahararren tauraron fina-finan Indiya Amitabh Bachchan, dansa Abhishek Bachchan, da surukarsa Aishwarya Rai Bachchan da kuma jikarsa sun kamu da cutar korona ranar 11 ga watan Yuli.

Riek Machar: Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu da matarsa Angelina Teny, wadda ke rike da mukamin ministar tsaro, sun kamu da cutar korona, a cewar sanarwar da ofishinsa ya fitar ranar 18 ga watan Mayu.

Tom Hanks: Fitaccen tauraron fina-finan Amurka wanda ya taba lashe kyautar Oscar Tom Hanks da matarsa, tauraruwa Rita Wilson, sun kamu da cutar korona a watan Maris. Dukkansu suna da shekara 63, kuma sun je Australia saboda fim din da Hanks yake yi a lokacin.

Maumoon Abdul Gayoom: Tsohon shugaban Maldivesya ce ya kamu da COVID-19 ranar 25 ga watan Agusta. A sakon da ya wallafa a Twitter, tsohon shugaban mai shekara 82 ya ce yana sa ran "warkewa da wurwuri da koshin lafiya" a gare shi da ma dukkan masu fama da cutar.

Kwaku Agyemang-Manu: Ministan Lafyar Ghana ya kamu da cutar COVID-19 "a yayin da yake kan aiki", amma yana cikin koshin lafiya, a cewar sanarwar da shugaban kasar ya fitar ranar 14 ga watan Yuni.

Idris Elba: Tauraron fina-finai kuma mawaki a Birtaniya ya ce ya kamu da cutar korana ranar 16 ga watan Maris a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, kodayake bai nuna wata alama ta kamuwa da cutar ba, amma ya killace kansa.

Wannan layi ne

Paul Pogba: Dan wasan Mancheter United Paul Pogba ya kamu da korona, in ji kocin ƙungiyar kwallon kafa ta Faransa Didier Deschamps, a sanarwar da ya fitar ranar 27 ga watan Agusta.

Dan wasan mai shekara 27 zai killace kansa na kwana 14.

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Paul Pogba shi ne ɗan wasan Manchester Utd mafi tsada wanda aka sayo a kan £89m

Usain Bolt: Fitaccen dan wasan tseren nan na duniya wanda ya lashe gasar Olympic sau takwas Usain Bolt ya kamu da cutar korona, a cewar sanarwar da ma'aikatar Lafiyar Jamaica ta fitar ranar 24 ga watan Agusta.

The Rock: Tauraron fina-finan Amurka Dwayne "The Rock" Johnson ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar 2 ga watan Satumba. Ya kara da cewa matarsa da 'ya'yansa biyu ma sun kamu da cutar kodayake sun warke kuma suna cikin koshin lafiya.

Yarima Albert: Yarima Albert na Monaco, mai shekara 62, ya kamu da cutar korona amma yanayin lafiyarsa "ba abin tayar da hankali ba ne," a cewar ofishinsa a sanarwar da ya fitar ranar 19 ga watan Maris.

Michel Barnier: A ranar 19 ga watan Maris ne babban mai shiga tsakani na Tarayyar Turai kan shirin Birtaniya na ficewa daga Tarayyar, Michel Barnier, ya ce ya kamu da COVID-19.

Wannan layi ne