Amitabh Bachchan: Shahararren ɗan Bollywood ya kamu da korona

Asalin hoton, @SrBachchan
Shahararren ɗan wasan fim ɗin Indiya Amitabh Bachchan ya kamu da cutar korona.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Bachchan ya bayyana cewa tuni aka tafi da shi asibiti kuma tuni 'yan uwansa da iyalansa da ma'aikatansa suka yi gwajin cutar.
Ya kuma yi kira ga waɗanda suka yi mu'amula da shi kwanaki 10 da suka gabata da su yi gwajin cutar ta korona.
Amitabh Bachchan ya shahara sosai a wasan fim ɗin Bollywood, kuma ya yi fina-finai da dama da suka ratsa zukatan masu kallo.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƙasar Indiya ita ce ta uku a faɗin duniya a yawan masu cutar korona da mutum 820,916, a ranar Asabar ƙarfe 9:00pm agogon BST.
Haka zalika mutum 22,123 cutar ta korona ta kashe a ƙasar.







