Donald Trump: An bankaɗo yadda shugaban Amurka ya yi ƙwauron biyan haraji

Shugaba Trump

Asalin hoton, Getty Images

Jaridar New York Times ta ce Shugaba Donald Trump ya biya dala ɗari bakwai da hamsin ne kacal kan harajin tarayya a shekarar da ya ci zaɓen shugaban ƙasar.

Jaridar ta ce ta samu bayanan biyan harajin shugaban na shekaru 20 bayan kwashe tsawon lokaci yana ɓoyewa.

Bayanan sun nuna cewa a cikin shekaru goma daga cikin shekaru sha biyar kafin ya hau kan mulki bai biya haraji ba kwata-kwata.

Jaridar ta ce bayanan sun nuna yadda Trump a matsayinsa na dan kasuwa ya rika tafka asara tsawon lokaci da kuma yadda ya rika kaucewa biyan haraji.

Ya rika nunawa mahukunta cewa bazai biya ba saboda asarar da yake tafkawa ta fi ribar da yake samu yawa sosai, nesa ba kusa ba.

Mista Trump ya yi watsi da rahoton a matsayin "labarin karya. "

Ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi cewa: "A gaskiya ina biyan haraji. Kuma nan ba da jimawa za ku ga haka idan na karbi takardun harajina - ana gudanar da bincke a kansu, an dade ana gudanar da bincike a kansu."

Ita dai Jaridar New York Times ta ce tana shirin wallafa jerin labarai game da takardun harajin na Trump gabanin zaben kasar na Nuwamba.

Wadanne abubuwa jaridar ta bankado?

Trump Tower

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban lauyoyin gamayyar the Trump Organization ya ce "galibin abubuwan da aka fada ba gaskiya ba ne."

The Times ta ce ta yi nazari kan takardun haraji na Shugaba Trump da kamfanoni mallakar iyalan Trump tun daga shekarun 1990s, da kuma harajin nasa na 2016 da 2017.

Ta ce shugaban ya bia harajin $750 kacal a 2016 da 2017, kuma bai biya haraji ba kwata-kwata a shekaru 10 cikin shekaru 15 da suka gabata, "saboda ya bayar da labarin cewa ana yin asara" a harkokin kasuwancinsa.

Mr Trump hamshakin dan kasuwa ne gabanin zamansa shugaban Amurka.

Si dai jaridar ta ce bayanan da ya bai wa hukuar haraji ta kasar "sun nuna shi a matsayin dan kasuwar da ke samun miliyoyin dala a duk shekara amma yana cewa yana yin asara domin zille wa biyan haraji".

Gamayyar harkokin kasuwancinsa mai suna the Trump Organization ta bi sahun shugaban kasar wajen musanta zille wa biyan haraji.

Shugaban lauyoyin gamayyar Alan Garten, ya shaida wa the Times cewa "galibin abubuwan da aka fada ba gaskiya ba ne.".

Tun shekarar 1970 shi kadai ne shugaban da ya boyewa 'yan kasar bayanan harajinsa, abin da wasu ke kallo a matsayin boye gaskiya.

Yayin da ya rage makonni biyar kacal a gudanar da zaben shugaban kasa, masu adawa da Mr Trump sun yi hanzarin yin Allah wadai da bayanan harajin nasa.

Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi, ta ce shugaban ya dauki matakai na ban mamaki domin kaucewa biyan kasonsa dai dai, yayin da Amurkawa dake aiki tukuru ke biyan nasu.

Har yanzu babu wani bayani da ya fito daga dan takarar shugaban kasar na Democrats, Joe Biden, amma kwamitin yakin neman zabensa ya bayyana cewa ashe dai malamai da masu kashe gobara da ma'aikatan jinya duk sun biya harajin da ya fi Mista Trump.