Taron Ecowas a Nijar: Buhari ya gargaɗi shugabannin kungiyar kan ta-zarce

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargaɗi shugabannin ƙungiyar ci gaban tattalin arzikin ƙasashen Afirika ta Yamma ECOWAS kan tsawaita mulkinsu yana mai cewa hakan babban hatsari ne.

Ya bayyana haka ne a Jamhuriyyar Nijar a yau Litinin inda shugabannin suka haɗu don tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi yankin.

Taron na kwana ɗaya, kuma shi ne irin sa na 57 kuma an gudanar da shi ne a Yamai, babban birnin ƙasar.

Taron ya tattauna kan yanayin da ake ciki a Mali bayan juyin mulkin da soji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ranar 18 ga Agusta lamarin da ya sa ECOWAS ta sanya wa ƙasar takunkumi.

Shugabannin ƙasashen Najeriya da Senegal da Cote d'Ivoire da kuma Burkina Faso na daga cikin mahalarta taron.

Abin da Buhari ya ce

Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya ya fitar ranar Litinin da la'asar ta ce Shugaba Buhari ya bukaci takwarorinsa na ECOWAS su daina tsawaita mulkinsu domin hakan "yana zama silar matsala".

"A matsayinmu na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS, akwai bukatar mu yi biyayya ga kundin tsarin mulki kasashenmu, musamman game da wa'adin mulki. Wannan fanni ne da ke haifar da rikici da dumamar yanayin siyasa a kasashenmu," in ji Shugaba Buhari.

Da alama Shugaba Buhari yana shagube ne ga shugabanni irin su Shugaba Alpha Conde na Guinea Bissau, mai shekara fiye da 80, wanda ya amince ya yi wa kundin mulkin kasar kwaskwarima yadda zai sake tsayawa takarar shugabannin kasarsa duk da tarzomar da aka kwashe wata da watanni ana yi.

Mahalarta taron sun kuma tattauna kan wani rahoto na musamman game da annobar cutar korona, wanda Shugaba Buhari ya gabatar a matsayinsa na Jagoran Yaƙi da Korona - kamar yadda shugabannin ƙasashe mambobin ƙungiyar suka naɗa shi ranar 23 ga watan Afrilun 2020.

Shi ma Shugaban Ƙasar Sierra Leone, Julius Maada Bio ya gabatar da rahoto na musamman kan kuɗin bai-ɗaya na Afirka ta Yamma da ake kira Eco -wanda ƙasashen ke yunƙurin samarwa - tare da Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast.

Ouattara, shi ne shugaban kwamitin kuɗin bai-ɗaya na Afirka ta Yamma mai suna West African Economic Monetary Union (WAEMU).