Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar Dinkin Duniya: Wane amfani Nijar za ta samu daga jagorantar kwamitin tsaro?
Jamhuriyyar Nijar za ta jagoranci kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, karo na biyu da ƙasar za ta samu wannan jagorancin bayan shekaru 40.
Kwamitin Tsaron na Majalisar Ɗinkin Duniyar na da alhakin samar da zaman lafiya da tsaro tsakanin ƙasa da kasa. Kwamitin na da mambobi biyar na din-din-din masu kujerar na ƙi, da kuma mambobi 10 na wucin gadi.
Mambobi biyar ɗin na din-din-din sun haɗa da China da Faransa da Rasha da Birtaniya da kuma Amurka.
Sai kuma mambobin na wucin gadi a halin yanzu akwai Belgium da Jamhruiyyar Dominican da Estonia da Jamus da Indonisiya da Nijar da Saint Vincent da Afrika Ta Kudu da Tunisia da kuma Vietnam.
Ƙasashen duniya dai na kallon Nijar a matsayin ƙasa mai muhimmanci da za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo zaman lafiya a yankin Sahel.
Shigar ƙasar kwamitin tsaro na MDD na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun matsananciyar matsalar tsaro a yankin Sahel. Makwaftan ƙasar sun sha fama da rikice-rikice wanda har yanzu ana kai, daga arewacin ƙasar akwai Libiya inda aka fara rikici tun zamanin marigayi Mu'ammar Gaddafi.
Daga kudu maso gabashin ƙasar akwai yankin Diffa da ke ta kusa da tafkin Chadi, wurin da masu iƙirarin jihadi kamar ISWAP da Boko Haram ke yawan kai wa hari.
Akwai kuma matsaloli na sauyin yanayi inda ake yawan samun ambaliyar ruwa a ƙasar da ke tilasta wa dubban mutane rasa muhallansu.
Shin wane alfanu Nijar za ta samu daga jagorantar kwamitin tsaro na MDD?
BBC ta tattauna da Dakta Abubakar Kari, wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum inda ya shaida wa BBC cewa alfanun da Nijar ɗin za ta samu ba shi da yawa amma ƙimarta za ta ƙaru a idon duniya.
Dakta kari ya bayyana cewa duk da Nijar za ta jagoranci wannan kwamiti na tsaro, "ba za ta iya sa wa ba kuma ba za ta iya hana wa ba", in ji shi. Ya ce ƙasashen da ke da kujerar din-din-din a kwamitin kamar su China da Amurka da Faransa su ne ma su wuƙa da nama kuma duk abin da suke so shi yake faruwa.
A cewarsa, abin da Nijar za ta iya yi shi ne: "Ta yi ƙoƙari a kawo maganar tsaro, misali na Boko Haram, ko kuma Azibinawa waɗanda a da suke yaƙarta.
"Ko da Nijar ta kawo irin waɗannan muhimman batutuwa sai waɗannan ƙasashe biyar masu kujerar din-din-din sun amince, sakamakon su ke da wuƙa da nama," in ji shi.
Ya ce kuma ko wane daga cikin waɗannan ƙasashe biyar za su iya sa wa a yi watsi da wani mataki ko kuma kudiri da za a ɗauka.