Mahaifi ya tara wa ɗansa kuɗin gida da kwalaben giya na shekara 18

Macallan whisky
Bayanan hoto, Duk shekara ake ba Matthew Robson kyautar kwalbar wiski mai shekara 18 a zagayowar ranar haihuwarsa wanda yanzu darajarsu ta kai fan £40,000

Mutumin da mahaifinsa ke ba shi kyautar giya duk shekara har tsawon shekara 18 don murnar zagayowar ranar haihuwarsa zai sayar da kyautukan da ya tara na giya don ya sayi gida.

Matthew Robson, daga Taunton, an haife shi a 1992 kuma mahaifinsa Pete ya kashe kusan fan 5,000 kan kwalaben giya 28 na Macallan.

Darajarsu yanzu ta kai sama da fan 40,000 - kwatankwacin naira miliyan 20 - kuma ya saka su a kasuwa.

Robson mai shekara 28 ya ce "watakila ba kyauta ba ce" ga yaro mafi kyau tare da umurni "mai tsauri cewa kada a buɗe".

Pete and Matthew Robson
Bayanan hoto, Pete Robson ya ce ba kwalbar giyar Wiski kawai yake ba ɗansa Matthew ba a ranar zagayowar haihuwarsa

"Duk shekara ina samun kyautar zagayowar ranar haihuwa," In ji Matthew. "Na yi tsammanin wata ƙaramar kyauta ce tun da ni ƙarami ne a lokacin da zan fara sha."

"Amma na kasance cikin umurni mai tsauri, kada na taɓa buɗe su kuma na yi iya ƙoƙarina kuma na yi nasara kuma dukkaninsu suna nan ba abin da ya same su."

Macallan whisky
Bayanan hoto, Matthew ya ce an ba shi umurni mai tsauri kada ya taɓa buɗe kwalbar giya da ake ba shi kyauta ranar zagayowar haihuwarsa

Mahaifinsa Pete. wanda ya fito daga Milnathort a Scotland, ya ce kwalbar giyar Wiski ta 1974 ta farko an saye ta don "busar da kan jariri."

"Na yi tunanin zai yi kyau idan na dinga sayen ɗaya duk shekara, inda zai samu kwalabe 18 na shekara 18 a yayin da yake cika shekara 18," in ji shi.

"Wannan ba ita kaɗai ce kyautar da ya samu ba daga gare mu. Kawai kyauta ce ta musamman amma ya yi sa'a mun ci gaba da yin kyautar."

Macallan whisky
Bayanan hoto, Dillalin wiski, Mark Littler, ya ce kwalaben sun ja hankalin mabuƙata daga New York da yankin Asiya

Tun lokacin yake tara kwalaben kuma Matthew yana fatan sayar da su kan fan £40,000 don ya yi amfani da kuɗaɗen ya sayi gida.

An sayar da su ta hannun dillalin Wiski Mark Littler, wanda ya bayyana su a matsayin "kammalallu."

"Darajar Macallan ta ƙaru a tsawon shekara 10," a cewarsa. "Samun jerin kwallaben hanyar ciniki ce mai kyau."

Ya ce sun ja hankalin masu buƙata daga New York da yankin Asiya.