Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tsadar fulawa ta sauya farashin burodi a Najeriya
Tsada ko karin kudin fulawa a daidai lokacin da ake kokowa da sauyin farashin kudin shinkafa na sake haddasa damuwa da fargabar yadda a kullum farashin abinci ke sake hauhawa a Najeriya.
A ƴan kwanakin nan, kuɗin burodi da duk wasu kayayyakin da ake hada wa na fulawa na sake kara kudi ba tare da sani dalilin ba.
Karin kudin ba wai ya tsaya kadai ba ne kan fulawa kusan ya shafi garin tuwo da taliya da alkama.
Wani mazaunin Kano, Ibrahim Sabo ya shaida wa BBC cewa ya yi mamaki da ya je sayen burodi aka shaida masa cewa farashin ya sauya.
Ya farashin fulawa yake a yanzu?
Wannan kari ba wai a wuri guda ba ne kusan a duk jihohi da birnin Tarayyar ƙasar an samu sauyin farashi idan aka kwatanta da makonin da suka gabata.
Adamu Abdulkadari manajan gidan burodin AMK Kore a Kano ya shaida cewa BBC cewa a baya suna sayen buhun fulawa kan dubu 10,000 amma yanzu farashin ya kai 13,500.
Adamu ya ce babu wani cikaken bayani da suka samu kan dalilin karin kudin fulawar, amma kamfanoni na ce musu komai ya kara kudi ne.
"Ba su ce mana takamaimai ga dalilin tsadar fulawar ba amma manyan diloli na cewa sinadarann hada kayan fulawa sun kara kudi'".
Abin takacin ma shi ne bayan ka siya fulawa mai tsada, shi ma sukari da hoda da yis da sauran kayan hada burodi duk sun yi kuɗi, in ji Adamu
Manajan ya ce sun tattaunawa a ƙungiyance kan tsadar amma da alama ba sauyi za a samu ba tunda tsadar ta tilasta dole a yi karin kuɗin burodin.
''A baya muna bada tallafi ko ragin kudin burodin amma yanzu mun daina, sannan wayanda basu kara kudi ba sun rage girmar burodin.
Karin bayyani
Burodi kusan abinci kowanne gida ne a Najeriya. Kusan ya fi kowanne abinci saurin samuwa. Cimakar gidan mai kudi da talaka.
Akwai gidajen burodi da dama a kasar da ke samar da ayyukan yi ga mutane da dama.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na cikin kasashe 'yan gaba gaba da al'ummar ba su da cimmaka sama da Burodi.
Sai dai ana ta'alaka tsadar da kayan fulawa ke yi da burin da kamfanonin suka sa kan fulawar da suke fitarwa.
Ana zargin cewa kamfanonin baki ƴan kasashen ketare da ke sarrafa da sanar da fulawa kusan su suka taka rawa wajen tsadar da kayan fulawa ke yi a kasar.
Ƴan Najeriya da dama na ganin idan mahukunta suka cigaba da zura ido kayan abinci na tsada to nan gaba ga mutane da dama abin kai wa baki zai gaggara.