Juyin mulkin Mali : ECOWAS ta umarci a kafa gwamnatin riko ta shekara daya a Mali

Masu shiga tsakani na kungiyar kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, sun fada wa shugabannin juyin mulkin Mali cewa za su amince da kafa gwamnatin rikon kwarya da zata kasance karkashin farar hula ko wani soja da yayi ritaya ta tsawon shekara daya.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito gwamnatin Najeriya na sanar da wannan mataki.

Sanarwar ta zo ne bayan ganawar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi da Good Luck Ebele Jonathan, wanda ke jagorantar shirin sasantawa karkashin kungiyar.

A ranar 18 ga watan Aprilu ne wasu sojojin kasar suka kifar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubakar Keita, kana suka yi awon gaba da shi zuwa wani sansaninsu, abin da kasashe da dama suka yi Allah-wadai da shi.

A farkon shekarar nan ne tsohon shugaban kasar ya fara gamuwa da tutsu daga jama'a da ke zargin gwamnatinsa da kasa shawo kan matsalolin da suka addabi kasar, kamar matsalar tsaro da kuma matsalar tattalin arziki.

Su kansu sojojin kasar na kokawa game da rashin biyansu albashi duk da kokarin da suke yi na kawar da masu ikirarin jihadi da ke ci gaba da tsananta kai hare-hare a wasu yankunan kasar.

Sanarwar na zuwa ne yayin da tarrayyar Turai ta dakatar da shirinta na horar da sojoji da 'yan sandan kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Wata sanarwa da Tarrayar Turan ta fitar ta ce an tsara shirin ba da horo ne ga gwamnatin da ta kira halattacciya.

Sojoji sun aiwatar da juyin mulkin ne sakamakon ƙaruwar da aka samu a yawan masu adawa da gwamnati a kan yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar da kuma tashin hankalin da ake fuskanta daga mayaƙa masu ta da ƙayar baya wadanda ke ci gaba da samun kafuwa a yankin Sahel.

Sai dai Faransa wadda take ta dubban sojoji a yankin tun daga shekarar 2013 lokacin da ta fatattaki mayaƙa masu ikirarin jihadi daga arewacin Mali ,ta ce ba za ta janye dakarunta daga kasar ba sakamakon juyin mulkin.