Ƙasar Sudan: Masu haƙar gwal ta haramtacciyar hanya sun lalata wurin tarihin da ya shafe shekara 2000

Masu hakar gwal ta haramtacciyar hanya sun lalata wani yanki mai tarihi da ya shafe kusan shekaru 2,000 a hamadar sahara da ke gabashin Sudan.

Jami'ai daga sashen al'adun gargajiya da kayan tarihi na kasar ta Sudan sun ce lokacin da suka ziyarci yankin mai nisan kilomita 270 daga arewacin Khartoum babban birnin kasar a watan jiya sun iske wasu masu hakar ma'adanai ta haramtacciyar hanya na tsaka da tono gwal.

"Babbar manufarsu guda daya ce tak, ita ce su samu gwal, sun yi barna a nan wajen sosai, sun rika amfani da manyan injina wajen hako gwal", in ji Habab Idriss Ahmed, wanda ke aiki a wajen tarihin tun 1999.

Sudan gida ce ga daruruwan Dala, da sauran wuraren tarihi, duk da cewa ba iri daya ba ne da Masar mai makwabtaka da ita.

Masu neman gwal ta barauniyar hanya sun lalata Sai, wani tsibirinmai nisan kilomita 12 da ke kusa da Kogin Nilu, wuri ne mai cike da kaburbura, amma duk da haka masu hakar gwali din sai da suka lalata shi.

Hatem al-Nour, daraktan al'adun gargajiya da kayan tarihi a kasar Sudan, ya ce, "An lalalta akalla wurare 100 cikin 1000 da aka sani da kuma wadanda ba a kai ga sani ba har yanzu

Ya kara da cewa: "Rashin cikakken tsaro a wuraren ne ke bada damar kutsawa don satar gwal din."

Sudan ce kasa ta uku a Afrika da tafi arzikin gwal, bayan Afrika ta kudu da Ghana.

Sannan bangaren na taimakawa gwamnati kwarai wajen samun kudin shiga, sai dai a yanzu akwai babbar barazana ga bangaren.

Har ila yau babu wata tursasawa ta ganin an bi dokar da ake da ita da ta hana jama'a shiga wurin don hakar ma'adanai.

"Kamata yayi a jefa su a kurkuku, sannan a yi gwanjon kayan aikin da suke amfani da su wajen hako gwal din, ai akwai dokokin da suka yi tanadin haka", in ji Mahmud Altayeb, wani mai bincike kan al'adun gargajiya a Sudan.

Daya daga cikin dabarun dogon lokaci na kare wuraren tarihi shi ne koyar da matasa labarin tarihin kasar Sudan, ta yadda za su iya mutunta ababensu, a cewar Farfesa Habbab Idris Muhammad, babban jami'in sa ido kan al'adun gargajiya a kasar.