Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sudan: Mutum 63 ne suka mutu a ambaliyar ruwa tun daga watan Yuli
Ƙasar Sudan ta ce mutum 63 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa tun daga watan Yuli sannan guguwa ta raba dubbai da mahallansu.
Gidaje 14,000 ne suka rushe da kuma gine-gine 119, yayin da wasu 16,000 suka lalace, a cewar alƙaluman hukumar tsaro ta farar hula wanda ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar.
Ana yawan samun ruwan sama mai yawan gaske tsakanin watan Yuni zuwa Oktoba a Sudan sannan kuma a fuskanci ambaliyar a kowacce shekara.
Ofishin ayyukan jin ƙai na OCHA da ke Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙiyasta cewa fiye da mutum 185,000 ne ambaliyar ta shafa sannan ta ce akwai yiwuwar ci gaba samun ruwan saman a watanni masu zuwa.
Jihohi 17 cikin 18 na ƙasar ambaliyar ta shafa, wadda ta haifar da zaizayewar ƙasa.
"Ana ci gaba da buƙatar kayan tallafi a Sudan yayin da ƙasar ke fama da bala'o'i daban-daban da suka haɗa da rikicin tattalin arziki da ambaliya da annoba," in ji OCHA.