Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump na son sasanta Isra'ila da ƙasashen Musulmi
Amurka ta ce tana sa ran Sudan za ta farfaɗo da hulɗa tsakaninta da Isra'ila, kamar yadda rahotanni daga Sudan suka nuna.
Jaridar Al-Jaridah mai zaman kanta ta ce yadda Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya nuna goyon bayansa ga sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan, wata manuniya ce da ke nuna Amurka za ta cire Sudan daga cikin jerin ƙasashen da ke tallafa wa ta'addanci.
Yadda Amurka ta shiga tsakani a sasancin da aka yi tsakanin Isra'ila da Daular Larabawa, za ta kuma jagoranci sasanci tsakaninta da Sudan.
Haka kuma za ta sasanta Isra'ila da ƙasashen Bahrain da Oman kamar yadda ministan leƙen asirin Isra'ila ya tabbatar ranar Lahadi.
"Bisa ga yarjejeniyar Isra'ila da Daular Larabawa, akwai kuma wasu ƙasashen yankin gulf da sauran ƙasashen musulmi da za a cimma yarjejeniya tsakaninsu da Isra'ila," inji Eli Cohen, ministan leƙen asirin Isra'ila.
Amurka ce ta jagoranci sulhu tsakanin Daular Larabawa da Isra'ila inda a ranar Alhamis, shugaba Trump ya sanar da cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu kan ɗage haramcin wayoyin salula tsakaninsu.
A baya dai, mutumin da ke a Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ba zai iya kiran wanda ke a Isra'ila ba.
Ministan sadarwa na Isra'ila, Yoaz Hendel, ya yi murna kan matakin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan ta ɗauka na cire wannan takunkumi, kuma ya ce ƙasashen za su amfana ta hanyar tattalin arziƙi.
A wata yarjejeniya da ƙasashen kuma suka saka wa hannu, sun amince kan wani batu da ke da alaƙa da gudanar da bincike kan cutar korona.