Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barakah: Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙaddamar da tashar nukiliya
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙaddamar da tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasashen Larabawa, a Gaɓar Tekun Persia.
An so a ƙaddamar da tashar nukiliyar tun a 2017, sai dai an ta yin jinkirin hakan sakamakon wasu dalilai na tsaro.
Tashar nukiliyar wadda aka yi wa laƙabi da Barakah, an yi ta ne domin biyan buƙatar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta hanyar samar mata da ɗaya bisa huɗu na lantarkin da ta ke buƙata ganin cewa akawai sauran hanyoyin da Daular ke samun wuta.
A makonni biyu da suka gabata ne dai Haɗaɗɗiyar Daular Larbawan ta tura tawaga ta farko zuwa duniyar Mars - wanda wannan shi ne yunƙuri na farko a kimiyance da wata ƙasa da ke yankin Gulf ta taɓa yi.
Baya ga nukiliya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan na zuba jari matuƙa kan hanayar samar da lantarki ta hasken rana -ganin cewa akwai rana matuƙa a yankin na Gulf.
Sai dai wasu masana kan harkar samar da wutar lantarki na dasa ayar tambaya kan wannan sabuwar tashar ta Barakah. Sun bayyana cewa samar da wutar lantarki ta hasken rana ya fi sauƙi da arha, kuma hakan ya fi dacewa da irin wannan yankin da yake cike da fargabar siyasa da kuma rikicin ta'addanci.
A shekarar da ta gabata dai ƙasar Qatar ta kira wannan sabuwar tashar nukiliyar a matsayin barazana ga zaman lafiya da kuma muhallin yankin.
Qatar dai za a iya cewa tamkar kishiya ce ga Saudiya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A dai yankin na Gulf akwai ƙasar Iran, kuma ana zaman doya da manja tsakanin ta da Amurka wanda har Amurkar ta sa mata takunkumi sakamakon shirinta na nukila mai cike da ruɗani.