Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An samu raguwar aikata laifuka da kashi 40 cikin 100 a Afrika Ta Kudu
Ministan 'yan sanda na Afrika Ta Kudu, ya ce an samu raguwar aikata laifuka da kashi 40 cikin 100 a lokacin watanni uku na farko da aka sa dokar kullen korona a ƙasar.
Bheki Cele, ya ce akwai raguwa a laifuka iri daban-daban da ake aikatawa ciki kuwa har da cin zarafi ta hanyar lalata.
A cewarsa, haramta sayar da barasa lokacin dokar kullen korona ya taimaka matuƙa wurin kawo raguwar aikata laifukan.
Sai dai Mista Cele ya ce hare-haren da ake kai wa shagunan sayar da barasa ya ƙaru a lokacin kullen.
Afrika Ta Kudu na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi aikata laifuka a duniya.
A wani bangaren kuma, ita ce ke da adadi ma fi yawa na masu ɗauke da cutar korona a nahiyar Afrika.
Sama da mutum 500,000 suka kamu da cutar korona a ƙasar, mutum 11,000 kuma cutar ta kashe, kamar yadda ƙididdiga ta nuna a ranar Juma'a.
Haramta sayar da barasa da taba sigari yayin dokar kulle a ƙasar ya jawo ce-ce-ku-ce.
Ƙasar ta saka wannan haramcin ne tsakanin 27 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Yuni. An sake saka dokar haramcin kuma tun daga 12 ga watan Yuli zuwa yanzu.
A lokacin da dokar ta fara aiki a watan Afrilu, Mista Cele ya yi gargaɗin cewa jami'ansa za su "lalata duk wani wuri da suka kama ana sayar da giya".
A watan da ya gabata ne Afrika Ta Kudu ta saki ƙididdigar laifukan da aka aikata a shekarun 2019/2020.
A shekarar da ta gabata, satar mota, fashi da makami, da kisa sun ƙaru matuƙa a ƙasar a ƙididdigar da aka fitar.
Cin zarafi ta hanyar lalata, tuƙin mota yayin da aka sha miyagun ƙwayoyi ko barasa da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba na cikin manyan laifukan.