Jubril Aliyu: Me doka ta tanada don kare haƙƙin yara a Najeriya?

Tun bayan da aka gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan abin da ta kira 'rashin imanin riƙon sakainar kashin da aka yi wa yaro', ɗan kimanin shekara goma mai suna Jibril Aliyu, hankulan 'yan kasar suka sake tashi kan irin cin zarafin da ake yi wa yara.

Kafin ɓullar labarin yadda kishiyoyin babar Jibril da mahaifinsa suka ɗaure shi a turken awaki tsawon shekara biyu a ranar Lahadi, a baya-bayan nan an yi ta samun rahotannin cin zarafin yara musamman ta hanyar fyaɗe a ƙasar.

Ko a ranar Talata da yamma ma rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba ta ce tana gudanar da bincike kan wani tsoho mai shekara sittin da bakwai da kuma ƙarin mutum biyu, bisa zargin killace wata yarinya 'yar shekara goma sha ɗaya, suka yi mata fyaɗe.

Wannan lamari ne ya sa BBC ta yi nazari na musamman kan waɗanne dokoki gwamnatin Najeriya ta tanada don kare haƙƙoƙin yara a ƙasar, ta hanyar tattauna wa da wasu masana haƙƙin ɗan adam da suka ƙware kan kare haƙƙoƙin yara a kasar.

Wane ne yaro da haƙƙoƙinsa?

Yaro shi ne mutumin da yake daga shekara ɗaya zuwa 14 sai kuma ɗan matashi daga 14 zuwa 17 a yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka fassara.

Dokokin ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa dole kula da yara sun haɗa da yin duk wani abu don ci gabansu a zahiri da tarbiyya da cinsu da shansu da kula da iliminsu (mai kyau) da lafiyarsu da walwalarsa.

Abba Hikima ya ce: ''Jihohi kamar Legas ma a Najeriya dole ne iyaye su bai wa 'ya'yansu ilimi ko kuma a gurfanar da su a gaban ƙuliya an bai wa kowa dama ya kai uban da da kara''

Sannan dokokin sun haramta dukan yaro ko yaya yake, amma dokokin Afrika ba su hana dukan yaro ba, ''sai dai dukan ka da ya zama wanda zai yi masa lahani,'' a cewar Abba Hikima.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce a kan ci zarafin yara a gidaje ko a cikin danginsu ko makarantu ko unguwanni da cikin al'ummomi da ma sauran wuraren da ake sa ran yaran z su kasance cikin aminci.

Hanyoyin cin zarafin yara sun haɗa da:

  • Dukansu ko ƙona su ko yi musu wani lahani a jiki ko yin jifa da su ko sanya musu guba ko ɗaure su
  • Cin zarafinsu ta hanyar lalata da su ko tattaɓa wasu ɓangarori na jikinsu da nufi a ji daɗi
  • Cin zarafin su ta hanyar takurawa ko razanarwa ko cuzgunawa ko tsoratar da su
  • Yin watsi da su ta hanyar banztar da su a hana su abinci ko sutura ko muhalli.

Dokokin da ke kare yaro a Najeriya sun bai wa yara kariya ta yadda ko sunansu ba za a faɗa ba a gaban kotu don kare martabarsu sannan an hana kotun hukunta su.

Barista Bulama Bukarti wani lauya ne mai kare hakkin ɗan adam a Najeriya, ya kuma ce akwai dokoki da gwamnatin tarayyar ƙasar ta tanada sai dai a Abuja kawai take aiki sai kuma wasu tsirarun jihohi da ba su wuce bakwai ba.

Abba Hikima ya ƙara da cewa: ''Yawancin jihohin arewacin Najeriya ba sa bin dokokin saboda akwai abubuwa da dama da suka ci karo da addini idan aka zo batun tarbiyyar yara, sai dai hakan ba ya nufin ba za su iya yi wa dokokin kwaskwarinma ba.''

Me doka ta tanada kan cin zarafin yara?

Barista Bukari ya ce akwai dokoki a matakai daban-daban sama da 10 kan hukuncin cin zarafin yara a Najeriya har a kundin tsarin mulkin ƙasar ma.

''Alal misali idan an zargi mutum da yin fyaɗe akwai mabambantan hukunci a jihohin ƙasar, a Kano da wasu jihohin ana yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ne ko ƙasa da haka kamar shekara 20 amma kar ya gaza haka.

''Sai dai akwai jihohi da dama da nasu hukuncin ɗaurin shekaru ne ƙasa da 4 inda su kuma alkalai suke amfani da wannan damar wajen yanke hukuncin shekaru kaɗan.''

Lauyan ya ci gaba da cewa akwai kuma laifuka irin babban aikin assha da mutum zai dinga tattaɓa yaro ko yarinya a wuraren da ba su dace ba, shi ma wannan hukuncin ɗauri ne, wasu kuma tara ko kuma a haɗa duka duka biyun.

''Laifi kuma irin na abin da ake zargin kishiyo sun yi wa ɗan mijinsu a Birnin Kebbi za a iya tuhumarsu da laifuka wajen huɗu ko biyar da suka haɗa da hana shi walwala da cin zarafin mutuntakarsa ta hanyar haɗa shi da dabbobi aka bautar da shi ta mumunar hanya.

To amma ba anan gizo ke saƙar ba, domin kuwa kamar yadda Bukarti ya faɗa ba a samar da dokokin matsala take ba, a wajen aiwatar da su take.

''Dole hukumomi irin su NAPTIP da 'yan sanda su tashi tsaye su tabbatar sun yi bincike mai kyau kan irin wadannan laifuka sannan a gurfanar a kotu da gaggawa, su ma kotuna su dinga yanke hukunci da wuri kar a tsawaita shari'ar.

''Sannan wajibi ne iyaye da hukumomi da jami'an tsaro da malamai da sarakunan gargajiya da masu faftuka su haɗa hannu wajen kawo ƙarshen cin zarafin yara da ake yi sakaka a Najeriya,'' in ji Bukarti.

Karin labarai masu alaƙa