Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fashewar sinadarai a Lebanon: Har yanzu ban ji ɗuriyar abokaina ba - ɗan Najeriya a Beirut
Wani dan Najeriya mazaunin birnin Beirut ya ce har yanzu bai ji duriyar abokan arzikinsa da dama ba bayan fashewar wasu sinadarai ranar Talata.
Hukumomi sun ce kusan ton dubu biyu da dari bakwai na Ammonium Nitrate ne ya yi bindiga lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 137 yayin da fiye da 5,000 suka jikkata.
BBC ta tattauna da wani dan Najeriya masaunin Lebanon wanda tsakaninsa da wajen da abin ya faru bai fi kilomita bakwai ba, sai dai ya nemi da a sakaya sunansa.
Za mu yi amfani da sunan (Shaheed) domin bayyana labarinsa da abin da ya ganewa idanunsa.
"Jiya [ranar Talata] mun ga tashin hankalin da ba mu taɓa gani ba anan - wasu da aka haifa a nan sun ce tun da suke a gabas ta tsakiya ba su taba jin fashewa irin ta shiya ba.
"Bayan fashewa ta farko mutane sun ta dakko wayoyi suna daukar hotuna amma ana samun fashewa ta biyu da yake ta fi karfi sai mutane suka fara zubar da wayoyinsu suna gudu domin tsira da rayuwarsu," in ji Shaheed.
Sai ya ce daga nan ne aka shiga dimauta babu wanda yake ta wani ko wa ta kansa yake domin tsira, wasu domin dimaucewa suka kai kansu ga halaka.
Da aka tambaye shi ko abin ya taba shi sai ya ce, "ina kusa da ofishin jakadanci na Kuwait abin ya faru gilasan kusa da mu dun sun fashe - A yanzu maganar da nake yi jina ya ragu domin kunnena ya ji karar fashewar, kuma hakan ya shafi jina".
Shaheed ya ce da mutane da dama ba su ga 'yan uwasu ba, yana mai cewa "ni ma akwai wadanda na sani amma ban gan su ba. Ban ji duriyar wasu abokan arzikina ba."
A cewarsa: "Babban asibitin Rafeeq Hariri aka rika kai mutanen da suka jikkata, wasu asibitocin ma su kansu fashewar ta shafe su."
Wannan fashewa ta zo ne cikin wani irin halin matsi da kasar take ciki, ba kawai na shawo kan annobar korona ba, har da matsalar tattalin arziki da ba a yi hasashe ba.
Wannan matsalar ta tattalin arziki ta jefa dubban mutanen kasar cikin matsanancin talauci ya kuma janyo wata gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati.