Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
#RevolutionNow: Ina dalilin zanga-zangar da ƙungiyar ke yi?
Jami'an tsaro a Najeriya sun damke gomman masu zanga-zanga a Abuja da Legas yayin wani maci da aka yi a biranen biyu ranar Laraba 5 ga watan Agusta.
A Legas, jami'an ƴan sanda sun tarwatsa ƴaƴan kungiyar da suka fita tituna a Ikeja, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye. A Abuja ma ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar har ta kai ga an kama wasu daga cikin mambobin kungiyar.
An kuma gudanar da zanga-zangar a wasu manyan biranen ƙasar.
Omoyele Sowore, wani ɗan jarida kuma ɗan siyasa wanda a bara ya tsaya takarar shugabancin Najeriya ne ya kafa ƙungiyar ta #RevolutionNow a 2019.
Mista Sowore ya tsaya takara ne a karkashin jam'iyyarsa ta Africa Action Congress, tare da shugaba mai ci Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da kuma wasu ƴan takara 70 inda ya zo na 10 da kuri'u 33,953 cikin kuri'u 28,614,190 da aka kaɗa wa dukkan ƴan takarar a zaben.
Bayan an fitar da sakamakon zaben, Mista Sowore ya bayyana rashin gamsuwarsa da sahihancin alƙaluman da suka ba Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa nasara a zaben.
Su wa ye ke zanga-zanga?
Omoyele Sowore ya kafa ƙungiyar RevolutionNow (wato #JuyinJuyaHaliYanzu) domin cimma wasu buƙatu na siyasa, wata kila domin bai sami nasara a zaben shugaban ƙasa da aka yi a bara ba.
Wani dalilin kuma shi ne jam'iyyun siyasa ba su da hurumin ɗaukar irin wannan matakin.
Sowore kuma mawallafin wata jaridar intanet ce mai suna Sahara Reporters, ya shirya wannan macin ne domin jaddada ranar 5 ga watan Agusta na kowace shekara ta zama ranar "nuna bacin rai" da kuma tunawa da ranar da kungiyar tasa ta fara fita bisa titunan wasu manyan biranen ƙasar a bara.
Shin me ƙungiyar ta ke so?
Kungiyar #RevolutionNow ta ce tana neman kawo sauye-sauye kan yadda ake tafiyar da sha'anin mulki a kasar baya ga rashin amincewar da ta ce ta yi da zaben shugaban kasa da aka yi a bara.
Ta rika yin kiraye-kiraye ga jama'ar kasar da su ɗauki matakin "hambare gwamanati mai ci ta Muhammadu Buhari", kuma shugaban ta Sowore ya ki amincewa da sahihancin zaben da shugaban na Najeriya ya lashe wanda ya ba shi damar mulkin Najeriya a wa'adi na biyu.
Mene ne dalilin yin zanga-zangar a wannan rana?
Mista Sowore da ƙungiyarsa sun ayyana ranar 5 ga watan Agusta a matsayin ranar nuna ɓacin rai kan abin da ya kira "rashin samar da daidaito a zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a watan Maris na 2019.
Ƙungiyar #RevolutionNow ta shirya zanga-zangar ta bana ce domin zagayowar ranar da ta fara zanga-zanga shekara daya da ta gabata. Ta ce fitowar ta wannan watan zai tabbatar da rashin amincewarta da abin da ta kira "mawuyacin halin da Najeriya ke ciki".
Ta ce tana son assasa wannan ranar ta zama ranar kwato wa Najeriya ƴanci daga yanzu har ranar da ta cimma nasara.
Wane martani gwamnati ta mayar?
A dalilin kiraye-kirayen da ya rika yi, hukumar tsaro ta cikin gida a Najeriya, DSS ta kama Mista Sowore kuma ta gurfanar da shi a gaban shari'a a bara. Ta tuhume shi da laifukan cin amanar ƙasa da halarta kuɗin haram baya ga wasu laifukan na daban.
Kakakin hukumar ta DSS Peter Afunaya ya bayyana dalilin kamawar da hukumar ta yi wa Mista Sowore:
"Yana yunkurin tayar da zaune tsaye, da hana zaman lafiya tsakanin al'umomin da ke cikin ƙasar nan saboda kiraye-kirayen da yake yi na juyin-juya-hali."
Me ke iya faruwa nan gaba?
Har daren Laraba, hukumomin Najeriya ba su fitar da wata sanarwa kan mataki na gaba da za su ɗauka kan kungiyar ta #RevolutionNow ba.
Sai dai ƙungiyar da wasu magoya bayanta sun shafe tsawon yinin suna ci gaba da gangami a shafukan sada zumunta, kuma suna cewa gwamnatin Najeriya na shirin mayar da ƙasar ta koma lokacin mulkin soja - lokacin da aka riƙa take hakkokin ƴan ƙasar.
Kuma baya ga mambobin ƙungiyar da ƴan sanda suka kama a Legas da Abuja, jami'an hukumar tsaron cikin gida ta DSS ta sake kama Olawale Bakare, wanda a bara aka gurfanar da shi tare da Mista Sowore a kotu domin fito-na-fiton da ƙungiyar ta yi da jami'an tsaro a bara.
Hukumar ta DSS ta kama Mista Bakare ne da wasu mutum shida a birnin Osogbo na jihar Osun yayin da suke gudanar da zanga-zangar ta #RevolutionNow.
Sai dai daga baya ƴan sanda sun saki wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka kama musamman a Abuja:
A bara wasu ƙungiyoyin kare hakkin dan Adam a ƙasar sun gamu da fushin hukumomin Najeriya saboda yada ta ce sun alakanta muradunsu da na ƙungiyar ta #RevolutionNow.
Ƙungiyar Amnesty International na cikin waɗannan ƙungiyoyin. Gwamnatin Najeriya ta sanya ta a gaba bayan da ta wallafa sakonnin kiraye-kirayen da ƙungiyar ta #RevolutionNow ke yi a shafinta na Tiwita.
A wani sakon da gwamnatin ƙasar ta wallafa a Tiwita, ta tuhumi Amnesty da rura wutar abin da ta kira yunkurin hambare tsarin mulkin Najeriya.