Coronavirus a Najeriya: 'Yadda zub da hawayena ya ceci ɗaruruwan malaman makaranta'

Asalin hoton, AFP
A cikin jerin wasikun da muka samu daga 'yan jaridunmu na Afirka, Wakilinmu a Kenya Joseph Warungu ya duba mana irin karamcin da ake nuna wa mutanen da ba su da karfi ko kuma suka shiga wata damuwa.
A lokacin da annobar korona ta bulla cikin kasashen Afirka, ta zamo babbar barazana inda wasu mutanen suka shiga cikin wani mummunan yanayi.
Malaman makarantun masu zaman kansu wadanda ke samun albashi saboda aikin da suka yi, sun sha wuya saboda rufe makarantu da aka yi wanda ba a san ranar budewa ba.
Yawancinsu sun koma gona, wasu kuma share-share sannan wasu kuma talla a kan tituna zuwa wani lokaci.
Wannan yanayi ya zamo abin da ba za a iya jurewa ba inda wasu har kuka suke a cikinsu kuwa akwai Akindele Oluwasheun da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Shi da sauran malaman makaranta sun saka ran cewa za a koma makarantu a watan Yuli a lokacin da gwamnati ta sanar da cewa za a bude saboda masu zana jarrabawa, amma sai aka fasa matakin da ya yi wa malaman makaranta ciwo sosai.
Akindele na da mace daya da 'ya'ya uku wanda dukkansu 'yan kasa da shekara takwas ne, ya shaida wa wakilin BBC a wayar tarho cewa, koda ya ji labarin ba za a bude makarantu ba, ya kadu sosai daga bisani kuma sai hawaye suka fara zuba a fuskarsa.
Ya ce: "Matata ta ce mini kada ka yi kuka, mu yi hakuri da yadda muka tsinci kanmu sannan mu lallaba a haka,to amma sai na fara tunanin wasu malaman wadanda basu da abin da zasu ciyar da iyalansu, ga wasu iyalan uwa da uban duk malaman makaranta ne wanda suak dogara da albashin makaranta wajen ciyar da iyalansu, ya za su yi ke nan?".
It was really difficult seeing elderly teachers who had given many years of service to the profession pleading for food"
Saboda ba zai iya jurewa halin kuncin da zai shiga da kuma wasu malamai ba, sai ya dauki wayarsa ya bayyana abin da ke damunsa ta hanyar dauka a bidiyo ya sanya a shafinsa na sada zumunta.
Ko da wani abokinsa ya ga wannan bidiyon sai ya bashi shawara a kan ya yada a sauran shafukansa na sada zumunta, nan ya aikata haka, biiyon kuwa ya zazzaga inda ma ba a zata ba har ma wasu a shafukansu na sada zumunta da suka taimaka wajen yadawa suka masa suna "Malamin makaranta mai kuka".
Akindele ya ce ya dauki wannan hoton bidiyon ne da nufin ankarar da mutane a kan su taimakawa malaman makarantu masu zaman kansu saboda basa samun albashi tun da aka rufe makarantu.
Wata 'yar jarida a Najeriya, Lara Wise, ta kaddamar da kampe a shafinta na Facebook domin neman Akindele tare da bukatarsa ya sanya bayanan asusun ajiyarsa na banki a shafinsa na Facebook.
Kan kace kwabo, kudade sun fara shiga asusun bankin Akindele daga ko ina a fadin duniya.
Saboda karamci irin na Akindele da kuma tausayim sai ya yanke shawarar ware fiye da naira miliyan daya da dubu dari biyu kwatankwacin fiye da da dala dubu uku domin taimakawa wasu malaman makaranta mabukata.
Ya ce ' Na ce da kai na tun da Allah ya jarabceni sannan ya bude mini hanyar samu, idan har na ci kudin nan ni kadi to ban kyautawa kai na ba tun da akwai da dama irina suna bukata'.
" Daga nan ne muka fara neman irin malaman da suke ta fadi tashi wajen ciyar da iyalansu, sai da muka samu fiye da 200, mun basu kayan abinci mai yawa ciki har da shinkafa da taliya, sannan mun kuma basu wani kudi don kashewa". Inji Akindele.

Asalin hoton, Akindele Oluwasheun Oladipupo
Sai da Akindele ya fara rabo kayan abinci ga malamai irinsa sannan ya gano irin matsalar da malaman makarantu masu zaman kansu ke ciki.
Malaman makarantu da ga ko ina a sassan Najeriya sai suka fara neman tallafi daga Akindele.
Ya ce " Abu ne marar dadi kaga tsohon malamin makaranta wanda ya jima yana koyarwa na neman abin da zai ci".
An yi ta mayar da martani kala-kala a shafin sada zumunta na Facebook inda ake ta magana a kan Akindele, wato malamin makaranta mai kuka, yayin da wasu kuma ke dora alhakin halin da irin wadannan malamai ke shiga a kan gwamnati saboda watsi da su.

'Allah ya yi wa Akindele albarka'
Wani dan Najeriya ya ce: "Tir da 'yan siyasar kasarmu wadanda ke ja mana masifu da dama, idan har mutum kamar Akindele zai fito ya taimaka wa mutane, ina ga masu kudinmu da 'yan siyasarmu da sai dai su ci su da iyalansu".
"Allah ya shi ma Akindele albarka, kuma Alah ya taimaki dukkan wadanda ke cikin kunci".
Akindele ya ce a gaskiya akwai mutane na gari a fadin duniya, domin na samu kudi daga wajen wadanda ba su sanni ba, ina mai matukar godiya a gare su".
'Damuwar dana shiga ta taimaka wa mutane da dama'
Wani dan kasar Kenya Michael Munene, ya samu yabo saboda yadda ya taimaka wa mutane a lokacin annoba.
Ya tashi a gidan da basa iya samun abincin da za su ci a rana guda, ya san yadda yunwa da talauci suke.
Koda ya girma ya fara neman na kansa ya zauna ne a gidan haya.
Ya shaida wa wakilin BBC wani abu da ya faru dashi da ya zame masa alkhairi.
Ya ce "Wata rana da safe mai gidan nake haya na jirana na gama amfani da bandaki wanda ke wajen gidan nake bayan na fito ya ce na fiya ya kulle gidansa wai don ban biya kudin haya ba".
"Haka na yi tsamo a waje ba bu kaya a jikina ba kuma kudi. Daga nan na sha alkwashin cewa ba zan taba bari a yiwa wani irin wulakancin da aka yi mini ba," in ji Micheal.
It's tough for my business but I can't bear the sight of homelessness"
A yau, Micheal na bayar da gidaje haya, idan har suka samu matsalar da ba za su iya biyansa haya ba, ya kan daga musu kafa har su samu.
Ya ce "Abu ne mai wuya a irin kasuwancin da nake yi, amma kuma ba zan iya ganin mutum zaune ba bu gida ba, tun a watan Mayu na fadawa wadanda ke gidajena da suka kai 30 a yanzu da su mayar da hankalinsu wajen neman abin da zasu ci ba wai tunanin biyana kudin haya ba".
A Accra babban birnin kasar Ghana ma, a lokacin dokar kulle Elizabeth Yawson ta taimaka wa mabukatan da ke gararamba a kan tituna.
Irin bajinta da taimakon da mutane irinsu Akindele da Micheal da kuma Elizabeth Yawson suka yi wa jama'a, yakamata ya zamo abin koyi ga sauran mutane domin a gudu tare a tsira tare, kuma duk abin da kayi idan har na alkhairi ne zaka gani a kaskonka haka idan ma na sharri ne.
People responded generously and we were able to feed about 100 people for one week"











