'Ba mu samu tallafin ciyarwar 'yan makaranta ba'

Asalin hoton, Getty Images
Wasu iyaye da BBC ta tattauna da su a kan batun tallafin ciyarwar 'yan makaranta da ministar ayyukan jin ƙai, magance annoba da bunƙasa rayuwar jama'a, Sadiya Farouƙ ta ce sun ba wa magidanta a Legas da Abuja da kuma Ogun, sun ce ba su gani a kasa ba.
Wata mata a jihar Legas da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce " Ni ban san da wani tallafin abinci da aka bayar ba, kuma ina da yara hudu dukkansu kuma 'yan makaranta ne wanda dokar kulle ta tilas ta musu zaman gida tsawon wata da watanni".
Itama wata mata Baraka Dahiru da ke tafiyar da wata kungiya da ke tallafawa mata da marayu a Legas ta ce, " Sam ban ji wani labari bama a kan wannan batu na bayar da tallafi, gashi kuma ina hulda da mabukata mata sosai, ba bu wanda ya ce mini ya samu wani tallafi".
Ba a jihar Legas ministar ta ce an bayar da tallafin ba, har da Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, inda anan ma BBC ta ji ra'ayin wasu magidanta a kan wannan batun tallafi.
Daya daga cikin magidanta a Abuja da shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce ko kadan bai samu wani tallafin abincin 'yan makaranta ba daga ma;aikatar jin kai, kuma yana da yara uku dukkansu 'yan makaranta.
Itama wata uwa a Abujan, ta ce 'ya'yanta biyar dukkansu 'yan makaranta, amma ba su ga komai ba a kasa.
Waiwaye

Asalin hoton, @SADIYA_FAROUQTWITTER
Wannan korafi na zuwa ne bayan da ma'aikatar ayyukan jin ƙai, magance annoba da bunƙasa rayuwar jama'a, ta ce ta kashe kimanin naira miliyan 523 da dubu 300 kan shirin ciyarwa a makarantu lokacin kullen cutar korona a ƙasar.
Ministar ma'aikatar Sadiya Farouk ce, ta bayyana hakan inda ta ce a Abuja, gida 29,609 ne suka amfana sai Lagos gida 37,589 yayin da gida 60,391 suka ci gajiyar shirin a jihar Ogun daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa ranar 6 ga watan Yuli.
Ta ce don bin umarnin shugaban ƙasa, ma'aikatarta ta tuntuɓi gwamnatocin jihohi guda uku inda suka amince da yin amfani da tsarin 'zubin abincin kai wa gida" a matsayin zaɓin ciyar da yara lokacin kulle.
Sadiya Faruƙ ta ce an kimanta kowanne zubin kwanon abinci a kan naira 4,200 bayan gudanar da cikakkiyar tuntuɓa.
Ministar ta ce don tabbatar da ganin an yi komai cikin gaskiya da amana, sun haɗa gwiwa da Shirin Samar da Abinci na Duniya a matsayin ƙwararrun abokan aiki.
Baya ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa irinsu EFCC da ICPC da hukumar tsaro ta DSS gami da wasu ƙungiyoyi don bin diddigin tsarin da ake gudanar da shirin.
To BBC ta tuntubi hukumar EFCC don jin irin rawar da ta taka wajen rabon wannna tallafi amma ta bakin wata babbar jami'a a hukumar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce basu san wannan labari ba, amma ba mamaki tsohon shugaban hukumar na da labarin ko akasin haka.











