Hajj 2020: Abubuwa 17 da mahajjatan duniya za su yi kewa a Hajjin bana

Bayanan bidiyo, Abubuwan da Mahajjatan bana suka yi kewa game da aikin Hajji
    • Marubuci, Halima Umar Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

A daidai irin wannan lokaci a kowace shekarar Musulunci, miliyoyin Musulmai ke taruwa a kasa mai tsarki don gudanar da ibadar aikin Hajji, wacce daya ce daga cikin rukunan addinin.

Sai dai a wannan shekara al'marin ya sha bamban, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, annobar cutar korona ta hana Musulmai daga sauran kasashen duniya samun damar yin aikin.

Hukumomi a Saudiyya sun kayyade cewa mutum 10,000 ne kawai za su yi ibadar ta bana kuma mazauna kasar ne kawai aka amincewa yin hakan ban da baki daga sauran kasashen duniya.

Hakan na nufin miliyoyin mutane da suka kuduri niyyar zuwa ibadar za su kasance cikin kewa ta ''da a ce ina Saudiyya yanzu da na yi kaza da kaza.''

Wannan ne ya sa BBC ta yi duba kan wasu muhimman abubuwa da mahajjatan duniya za su yi kewa a Hajjin ta bana.

Wannan layi ne

1.Hawan Arfa

Hawan Arfa shi ne jigo na aikin Hajji, wanda idan babu shi to hajjin ba ya ta kammaluwa. Ana yin hawan Arfa ne a ranar 9 ga watan Zul Hijja, inda a kan fita tun kafin ko bayan sallar Asuba. Ana dai so a fita kafin rana ta fito.

Mahajjata na wuni zur a wajen suna gabatar da addu'oi da zikirai da karatun kur'ani. A kan bar filin Arfah kafin rana ta fadi.

Hakika yinin filin Arfa na sanya nutsuwa a zukatan masu ibada, don haka dole mahajjatan da suka yi niyya bana su ji ina ma a ce suna can su samu albarkar wannan yini.

Short presentational grey line

2.Kwanan Muzdalifa

Filin Muzdalifa shi ne wajen da alhazai ke wucewa bayan an sauka daga Arfa. Fili tarwal babu tanti babu dakunan kwana. A nan ne duk girman mukaminka za ka gane dai-dai kake da sauran bayin Allah masu ibada a wajen.

Ana so a kwana a wannan fili sai dai ga tsofaffi da mata da marasa lafiya ne kawai za su iya barin wajen cikin dare.

A filin Muzdalifa ne ake dibar duwatsun da za a jefi shaidan da su washegari. Lallai dole wannan kwana mai matukar muhimmanci da ke kara wa mutum yakana da tsoron Allah ya kasance wani abin kewa a zuciyar maniyyata na bana.

Muslim pilgrims walk around the Kaaba (Tawaf al-Wadaa), Islam's holiest shrine, at the Grand Mosque in Saudi Arabia's holy city of Mecca on February 27, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda musulmi daga sassa daban-daban suke zagaye Ka'aba
Short presentational grey line

3.Jifan Shaidan

Da an yi sallar Asuba sai a kama hanyar tafiya Jamrah, wato wajen da za a jefi shaidan. Mafi yawan mutane kan tafi ne da kafa daga Muzdalifa duk da nisan da ke tsakanin wuraren biyu.

Amma da yake abu ne na bautar Allah ba lallai ka gane irin nisan tafiyar da ka yi ba ma.

A kan samu turmutsutsu a wasu lokutan amma hukumomin kasar na aikin fadada wajen kusan duk shekara wanda hakan ke rage cunkoso. Sannan ga wasu na'urori da ke fesawa mutane ruwa tun a kan hanya don rage musu tsananin zafin da ake ji.

Wayyo ko ni ma a yanzu da nake rubutun nan na ji kewar wannan aiki mai dumbin lada duk da cewa duk a hajjina na farko har suma na yi a wajen, a na biyun kuwa faduwa na yi ban suma ba amma na fita hayyacina.

Ana shafe kwana uku zuwa hudu wajen zuwa jifan shaidan.

Short presentational grey line

4.Zaman Mina

A ranar 8 ga watan Zul Hijjah ne ake fita Mina don fara ainihin aikin Hajjin.

Gaskiya rayuwar zaman Mina na kwanaki hudu na cike da dumbin aikin lada da kuma koyon darasi na rayuwar duniya. Daga cikin abubuwan da za a yi kewa dangane da wannan waje akwai ayyukan ibada da suka hada da zikirai da nafilfilu da sallolin jam'i da karatun kur'ani da zuwa jifan na tsawon kwanakin da za a yi a wajen.

Mina ne wajen da ake haduwa da mutane ta yadda ba lallai ka hadu da wadanda ka sani a Makka ko Madina ba amma Mina ta zama tamkar mahada.

Ina kewar zaman Mina kuma na san dukkan maniyyata na bana ma na kewar wajen.

Short presentational grey line

5.Dawafi

Farin gani ido da ido da Ka'aba sai a Dawafi. Dawafi ana fara yin sa ne da zarar an shiga birnin Makkah ba sai an fita Mina ba.

Ana fara yin dawafin Umara, sannan akwai dawafin ranar Sallah da ake kira Dawafil Ifada, sai kuma dawafin bankwana bayan an kammala aikin Hajji a lokacin da mahajjata za su koma garuruwansu.

Lallai dole ma mahajjata su yi kewar dawafi saboda irin shaukin da ke cikinsa. Ga ka ga Dakin Allah, me ya fi wannan dadi. Ga irina mai raunin zuciya kuka na kan yi idan ina dawafi, don ji na ke babu wani shamaki tsakanina da Mahaliccina a badini.

Vastly reduced visitor numbers circle the sacred Kaaba at Mecca's Grand Mosque

Asalin hoton, ABDEL GHANI BASHIR

Short presentational grey line

6.Sa'ayi ko Safa da Marwa

Safa da Marwa ibada ce da ke tafe hannu da hannu da dawafi, don idan aka yi dawafan nan in dai ba na nafila ba sai an biyo bayansu da Sa'ayi.

Safa da Marwa ibada ce da ake tafiya ana gabatar da adduóí a cikinta. Sannan za ta dinga sa ka tsoron Allah da tunanin haka Nana Hajara matar Annabi Ibrahim AS ta dinga yi lokacin da take nemar wa jaririnta Annabi Ismaíl ruwa don ya sha.

Lallai wannan ibada dole maniyyata su yi kewarta.

Short presentational grey line

7.Madina Masallacin Manzon Allah SAW

''Yaushe za mu Madina 'yan uwa, zuciyata ta ki dangana ga idanu na zubar ruwa, yaushe za mu ziyara dausayin sabunta shakuwa….,'' in ji wani mawaki mai suna Hafiz Abdullah.

Lallai kam zuwa ziyara Madina ka samu kanka a Masallacin Maznon Allah SAW babban al'amari ne mai tsayawa a rai. Shiga Rauda da ganin Mumbari da ganin Kabarin Manzon Allah SAW, lallai wadan nan manyan al'amura ne masu tsayawa a rai. Dole maniyyata su yi kewar wannan lamari.

Daga nan kuma alhazai za su karasa wajen Makabartar Baki'a inda mafi yawan sahababi da matan Manzon Allah SAW ke kwance don ziyara.

Muslim pilgrim join one of the Hajj rituals on Mount Arafat near Mecca (11 September 2016)

Asalin hoton, AFP

Short presentational grey line

8.Uhudu

Ziyara zuwa Dutsen Uhudu na daya daga cikin abubuwan da za su dinga tsayawa maniyyatan da ba su samu zuwa hajji ba a bana. A nan ne za a zagaya da alhazai don su ga kaburburan sahabban Manzon Allah SAW da aka kashe a Yakin Uhudu.

Short presentational grey line

9.Masallacin Quba

Ziyara zuwa masallaci na farko da Manzon Allah SAW ya fara yin sallah a cikinsa lokacn da ya isa Madina yayin hijirarsa.

A kan yi sallah raka'a biyu a yi addu'oi sannan a koma cikin Madina. Gaskiya zuwa Quba ma abu ne mai dadi da tsayawa a rai.

Short presentational grey line

10.Mikati

Idan daga Madina ka fito za ka tafi Makkah don fara ibadar aikin Hajji to mikatinka yana Zul Hulaifa ne. Idan daga Jeddah ne kuwa to a nan din za ka dauki mikatin haramar Umara ko na Hajji da Umarar, ya danganta da irin hajjin da za ka yi.

Ba abin da na fi tunawa irin wankan daukar niyya da ake yi a buga layi a gaban bandakunan, na maza daban na mata daban. Idan an fito wanka sai a saka ihrami a shiga mota a fara talbiyya ana ''Labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik…,'' har sai an shiga Makkah.

Short presentational grey line

11.Tafiyar mota

Wata makaranta ce mai zaman kanta da za a yi kewa. Ko dai daga Makkah zuwa Madina ko daga Madina zuwa Makkah ko kuma daga Jiddah zuwa Makka ko Madina ya danganta da yadda tsarin tafiyarka ya kasance.

Amma dai idan ana wucewar nan za ka yi ta rayawa a ranka ko nan wajen yaya yake a zamanin Annabi SAW? Sannan a kan tsaya a kananan garuruwa don yin sallah da cin abinci, abin dai gwanin dadi.

Short presentational grey line

12.Ruwan zamzam da dabino

Duk da cewa a yanzu haka a kowace kasa idan kana so za ka iya sayen zamzam da dabino, amma ba dai kamar a ce kana gindin maganin ba, inda famfo kawai za ka bude a cikin Masallacin Harami ka sha iya shanka. A Madina ma ga shi nan an zuba a tuluna na zamani a sha a koshi. Dabino kuwa ai ko ba komai za ka yi tsarabar Ajwa mai yawa daga Madina.

A Muslim pilgrim reads a copy of the Koran, as he joins one of the Hajj rituals on Mount Arafat (11 September 2016)

Asalin hoton, AFP

Short presentational grey line

13.Sayayya

Bayan ayyukan ibadah alhazai kan kashe kwarkwatar idanunsu ta hanyar shiga shaguna don sayen tsarabobin da za su kai wa 'yan uwa da abokan arziki. Kaya ne iya dibarka dole kar bar saura a inda ka gan su.

Da wahala ka shiga lungu ko sakon da ba za ka ga shaguna ba. Sannan ga rukunin shaguna na zamani a cikin manyan otel-otel din da ke daf da Harami inda ko baka sai komai ba dole a bai wa ido hakkinsa.

Watakila bana da na je da na sayo kallo-kallo.

Short presentational grey line

14.Shinkafa kaza da tuwon takari

Allah Ya bar mana shinkafa kaza. A gaskiya na san mafi yawan maniyyata na bana za su yi kewar cin shinkafar nan da ake juye ta a leda a dira mata bankararriyar kaza a matsa mata lemon tsami. Wayyo, garin dadi na nesa.

Sai dai wasu alhazan duk da dadi irin na shinkafa kaza su sun fi son cin abincin mutanenmu mazauna can irin su tuwo da sauran su.

Amma ni dai Allah na gani na fi son cimar Larabawa.

Short presentational grey line

15.Laban

Garin dadi na nesa. Duk da cewa akwai yogot kamar yadda aka fi sanin Laban da shi a kasashenmu, to gaskiya na Saudiyya daban yake.

Na san ba ni kadai ce zan yi kewar Laban ba muna da yawa.

Muslim pilgrims join one of the Hajj rituals on Mount Arafat near Mecca (11 September 2016)

Asalin hoton, AFP

Short presentational grey line

16.Karbar sabil

Bar batun girman mukami ko matsayi, a wasu lokutan dole ka samu kanka a karbar sabil kai ni kam ma dai ina da sha'awar karbar sabil dinnan don kuwa kayan dadi ne masu kudin Larabawa ke cika leda da su ana rarrabawa bayin Allah da sunan sadaka.

Ba dai na shiga rububin karba amma da an ba ni nake amshewa ina Allah Ya karba. Bana kam na san ba masu karbar ba kawai su ma masu rabawar sai sun yi kewar rashin rabawa da yawa.

Short presentational grey line

17.Mu hadu a gaban Darut Tauhid

Kalmar mafi yawan mutane kenan idan suna son yin mahada da 'yan uwa ko abokansu a bakin Masallacin harami. Gaban katafaren otel din Darut Tauhid ya zama matattara dumbin mutane a lokacin aikin Hajji.

Da Allah Ya yi zuwanmu a bana da sai dai na yi wa abokan aikina Bara'atu ko Umaymah da muka yi niyya tare waya na ce to mu hade a gaban Darut Tauhid bayan Sallar La'asar. Daga nan sai mu wuce KFC cin kaza da dankali.

Watakila na manta ban sanya wasu abubuwan da maniyyata za su yi kewa ba, amma dai na san na tabo muhimman da kowa zai iya yarda da ni cewa sun isa saka mana kewar wannan ibada mai dadi da dumbin lada.

Allah Ya sa muna da rabon zuwa badi.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta