Mayakan Boko Haram 155 sun tuba a Kamaru

Wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram da mabiyansu 155 a Kamaru sun yanke shawarar ajiye makamai domin su koma tafiyar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.
Hukumomi a lardin arewa mai nisa ne suka bayyana wannan yunkuri na 'ya'yan wannan kungiya.
Rahotanni sun ce wadannan mutane da suka kunshi maza da mata da matasa na zaman wucen-gadi ne a sansanin dakarun tsaro na hadin gwuiwa da ke garin Meri.
Daga cikin wadanda suka ajiye makaman akwai maza 87, mata 28 da kuma matasa 41.
Gwamnan Lardin Arewa mai nisa, Midjinyawa Bakary, ya kai wa tubabbun ziyara a garin Meri inda aka ajiye su, a cewar wakilin BBC da ke Kamaru.
Kazalika gwamnan ya musu alkawarin cewa gwamnati za ta ba su kulawar da ta kamata.
Ya ce za a nemi sanya su a guraban sana'o'i kamar kiwo, noma, gini, da kuma dinki wanda akasarin mata 28 da suke cikin wannan ayari sana'ar da suke yi kenan tun farko suka bari suka shiga jerin mayakan Boko Haram.
A wani taron da Gwamnan ya shugabanta a garin Meri tare da masu fada a ji na garin, dai-daikun jama'a sun bayar da shawara game da yadda za a ba wa wadannan mutane kula.
Dangane da batun noma wasu sarakunan gargajiya biyu na garuruwan Meri da Godola sun bada kyautar kasar noma ko wanne mai fadin kadada 15 a matsayin taimako.

Asalin hoton, Getty Images
Ba wannan ne karon farko da 'ya'yan wannan kungiya ke ajiye makamansu su tuba, sun sha yin hakan.
Ko a ƙarshen makon da ya gabata hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayar da sanarwar cewa gwamnati na shirin yaye tubabbun 'yan Boko Haram 603 bayan ta gama ba su horon sauya musu tunani











