Eid el Kabir 2020: 'Shekara 29 ban yi Sallar Layya a gida ba sai bana'

Asalin hoton, ANADOLU/GETTY IMAGES
Wani ma'aikaci a hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, ya shafe shekara 29 bai yi sallar layya a gida ba sai a bana.
Mutumin wanda muka sakaya sunansa, ya ce dalilin shafe wadannan shekaru bai yi layya a gida ba, saboda tun shekarar 1991 da ya fara aiki a hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya yake zuwa aikin Hajji.
Ya ce a bana ne kadai saboda bullar cutar korona da kasashen duniya ba za su aikin Hajji ba, shi ne zai yi sallar layya a gida.
''Wallahi duk ji na nake kamar ba ni ba, saboda na saba duk shekara a lokaci irin wannan muna cikin shauki na tafiya ko ma mun riga mun tafi, amma a yanzu ga shi cikin hukuncin Allah muna nan a NAjeriya babu batun zuwa Hajji.
''Ina kewar irin yadda nake dawainiya da alhazai tun daga Najeriya har a kammala aikin Hajji a kasa mai tsarki. Wannan abu ne da ke sa min farin ciki don shekarun da na shafe ina yi,'' in ji shi.
Mutumin ya ce, ''Ko da na je sayan ragon layya, kasawa na yi, kusan dukkan abokaina duk sun sayi ragon layyarsu, amma ban da ni, na kasa saya har yanzu.''
Ya ce, ''A kullum idan n aje gida sai an tambaye ni ina ragon layya, sai na ce a yi hakuri zan saya ai lokaci ba kure ba tukunn.''
''Ji nake wani iri kamar ba sallah ba saboda rashin sabo, tun da a irin wannan lokacin ina can a Saudiyya sai dai na yi hadaya kawai, inda ko ganin naman ba ma yi.
''Yanzu kam sai dai na bayar a yanka min ragon don ban taba yi da kaina ba.''
Mutumin ya ce "Ba mamaki Allah (SWA), ya kaddaro hakan ne saboda mu san irin rayuwar da kasarmu ko iyalanmu ke ciki a lokacin layya.''
Ya ce ya manta ma yadda ake yanka rago, don bai taba yanka rago ba sai dai ya bayar a yanka masa.
Ya ce, yanzu yana kewar yadda ake aikin Hajji saboda sabo, da kuma irin hada-hadar da ake da alhazai musamman 'yan Najeriya.

Ko ta manta yadda ake suyar naman layya?
Ita ma Fatima Muhammad Mustapha, shugabar yada labarai a hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, ta manta lokacin da ta yi Sallar Layya a gida Najeriya.
Ta ce, ''Saboda a shekarun baya kamar i yanzu muna can a Makkah saboda shirye-shirye da ma kula da yadda alhazan Najeriya za su gudanar da ibadarsu, da kuma tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ake so ba tare da matsala ba'.
Hajiya Fatima, ta ce ta manta rabon da ta yi aikin suyar naman layya saboda a can Saudiyya idan suka yi hadayar ba ma sa ganin naman don sadakar da shi ake yi zuwa kasashe masu fama da matsalar karancin abinci.
''Na dai tanadi kasakena na suya da duk kayan aiki, kuma ina da masu taya ni. Bana zan kokarta na yi abin da na dade ban yi ba tun da dama aikina ne a matsayina na mace.
''Ina kuma fatan suyata za ta yi dadi sosai.''











