An kashe manoma 20 a yankin Darfur na Sudan

'Yan bindiga sun kashe a ƙalla mutum 20 lokacin da suke koma wa gonakinsu karon farko cikin shekaru cewar wasu rahotanni daga yankin Darfur na ƙasar Sudan.

An kuma ce ƙarin mutum ashirin sun ji raunuka a harin da aka kai yankin Aboudos, mai nisan kilomita 90 kudu da Nyala, babban birnin lardin Darfur ta Kudu,

Yankin Darfur na fama da rikici kimanin tsawon shekara ashirin.

Faɗa tsakanin 'yan tawaye da dakaru masu biyayya ga tsohon shugaba Omar Hassan al-Bashir ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, an kuma kashe ƙarin wasu dubban ɗaruruwa.

A bara ne aka tumɓuke al-Bashir daga kan mulki, lamarin da sabunta fatan samun sauyi.

Sai dai har yanzu ayyukan tarzoma, ruwan dare ne a yankin Darfur.

Wani jagoran al'umma ya faɗa wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa mutanen da harin baya-bayan nan ya ritsa da su manoma da aka tilasta tserewa daga gonakinsu a shekarun baya.

Daga bisani an ba su damar koma wa gidajensu ƙarƙashin wata yarjejeniya da sabuwar gwamnatin Sudan ta cimma, amma sai kawai 'yan bindiga suka auka musu.