Coronavirus: An sauke gwamnan da ya dage sai an yi sallar jam'i

Firai Ministan Sudan Abdalla Hamdok ya sauke gwamnan babban birnin kasar, Khartoum, bayan ya bijire wa dokar hana yin sallar jam'i wadda gwamnati ta yi domin dakile yaduwar cutar korona.

Janar Ahmed Abdun Hammad Mohammed ya ki aiwatar da matakin da aka dauka na haramta yin sallah a masallatai da kuma ibada a coci-coci wacce za ta soma aiki ranar Asabar.

Ya zuwa safiyar Juma'a, an tabbatar mutum 32 na dauke da cutar korona a Sudan, yayin da mutum biyar suka mutu, sannan mutum hudu suka warke.

Tun da fari, ranar Alhamis 'yan sanda sun fesa barkono-tsohuwa kan masu goyon bayan hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir.

Sun yi zanga-zangar ne domin adawa da matakin da gwamnatin rikon kwarya ta dauka na aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.