Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugabannin ECOWAS ba su iya sasanta rikicin siyasar Mali ba
Shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma sun kammala wani taron ƙoli na wuni guda a Mali jiya Alhamis, ba tare da kwantar da ƙurar rikicin siyasar da ke ƙara ta'azzara a ƙasar ba.
Jagororin lardunan ƙasar Mali biyar ne suka gana da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da kuma jagororin adawan ƙasar masu shirya zanga-zangar neman sai shugaban ya sauka daga mulki, yayin da dogon rikicin masu iƙirarin jihadi ke barazanar jefa Mali cikin hargitsi.
Shugaban Jamhuriyar Nijar kuma shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) Mahamadou Issoufou ya ce "Manufar, ita ce lalubo hanyar yin sassauci da za ta ba da damar kawo ƙarshen rikicin Mali cikin hanzari.
Kuma (duk da haka) ina da kyakkyawan fatan cewa za a samo masalaha."
Shugaba Issoufou ya kuma bayyana cewa an tsara gudanar da wani ƙarin taron cikin makon gobe.
"Amma mun yanke shawarar gabatar da rahoto ga dukkanin shugabannin ƙasashen ECOWAS, a wani ɓangare na babban taron ƙolin da aka tsara gudanarwa ranar Litinin 27 ga watan Yuli.
A cewarsa sai a ƙrshen wannan taro ne, shugabannin ƙasashen ECOWAS za su ɓullo da wasu ƙararan matakai don tallafa wa ƙasar Mali