Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa zuwan Buhari Mali ya fusata wasu 'yan Najeriya?
'Yan Najeriya da dama na ce-ce-ku-ce kan tafiyar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi zuwa ƙasar Mali.
A ranar Alhamis Shugaban ya tafi ƙasar domin kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubakar Keita da kuma 'yan adawa a ƙasar.
Sai dai da alama jama'a da dama a shafukan sada zumunta sun fusata kan wannan tafiya ta shugaban, duk da cewa wannan ita ce tafiya ta farko da shugaban ya yi tun bayan da aka fara kullen korona a ƙasar.
Abin da jama'a suka fi mayar da hankali a kai shi ne shugaban ya je sasanci a daidai lokacin da ƙasarsa ke fama da rashin tsaro, sai kuma wasu na ce-ce-ku-ce sakamakon wannan ne karo na farko da aka ga shugaban ya saka takunkumi domin rufe fuskarsa.
Inuwar Giginya
Wasu masu sharhi a shafukan sada zumuntar na siffanta shugaban da inuwar giginya, wadda Hausawa ke fassara ta da "na nesa ka sha ki".
'Yan ƙasar suna zargin cewa rikice-rikice na faruwa a sassa daban-daban na Najeriya bai je ya yi sasanci ba amma ya tafi Mali.
@ayemojubar a Twitter ta bayyana cewa shugaban yana hanyarsa ta zuwa Mali a daidai lokacin da ake rikicin cikin gida ta jam'iyyarsa da kuma Najeriya baki ɗaya.
@hadd1nzarewa ya bayyana cewa shugaban bai kashe wutar rikicin wasu jihohin ƙasar ba amma ya tafi ƙasar waje.
'Yan Najeriyar sun daɗe suna zargin cewa shugaban ƙasar ya kasa magance rikicin da ake yi a ƙasar.
An shafe fiye da shekaru 10 ana rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya musamman jihar Borno.
A 'yan shekarun nan kuma akalar rikicin ta karkato zuwa arewa maso yammacin ƙasar inda a halin yanzu jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna ke kan gaba a cikin jihohin da 'yan bindiga ke cin karensu ba babbaka.
Buhari ya saka takunkumi
Wani lamari kuma da 'yan Najeriya ke ce-ce-ku-ce a kai a shafukan sada zumunta shi ne kan batun takunkumin da shugaban ya saka a karon farko a tun bayan ɓullar cutar korona.
Shugaban dai ya saka takunkumin ne a ranar Alhamis a hanyarsa ta zuwa Mali. Sai dai wasu 'yan ƙasar na yi masa shaguɓe kan lamari.
Sani Mainaira a Twitter ya bayyana cewa shugaban ya kasa saka takunkumi a lokacin da yake a Najeriya amma ya saka a lokacin da ya tafi wata ƙasar.
Shi ma Bello a shafin Twitter ya ce a karon farko shugaban ya saka takunkumi.
Dalilin Buhari na zuwa Mali
Malam Garba Shehu babban mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari ya shaida wa BBC cewa Shugabannin na Ecowas za su tattauna ne da ɓangarori masu rikici a Mali bayan tawagar Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan sun kasa gano bakin zaren warware rikicin.
Ya ce zuwan shugabannin na iya tasiri ga warware rikicin - "watakila za a dubi kima da darajarsu a matsayinsu na shugabannin kasashen yammacin Afirka a saurare su domin kwantar da fitinar tare da tabbatar da zaman lafiya a Mali".