Muhammadu Buhari: Shin gwamnatinsa ta gaza kare rayukan 'yan Najeriya?

Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasar a yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

A sanarwar da kakakin Amnesty International, Malam Isa Sanusi, ya aike wa manema labarai ranar Litinin, kungiyar ta ce "Rashin tsaro yana ci gaba da watsuwa a wani bangare na arewacin Najeriya; Katsina, Kaduna, Borno, Benue da wani yanki na jihar Niger, inda 'yan bindiga suke kashe mutane kullum, sannan su sace wasu, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mazauna kauyuka.

"Gazawar hukumomi wajen daukar matakin da zai kawo karshen wadannan hare-hare ta sa 'yan bindigar na cin karensu babu babbaka a wasu jihohin, kuma wannan lamari yana ci gaba da ta'azzara," in ji Amnesty International.

Kungiyar ta kara da cewa wadannan hare-hare sun sanya mazauna yankunan sun bar komai a hannun Mahalicci, inda kullum suke kwana su kuma tashi suna fargabar kai musu hare-hare.

Amnesty International ta nanata kira-kirayen da take yi wa gwamnati da ta mayar da kare rayukan jama'a ya zama babban abin da ta sanya a gaba.

Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai 'yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.

Gwamnatin kasar ta sha cewa jami'an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron 'yan bindiga ne, ko da yake 'yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne.