Da gaske Hadi Sirika ya yi barazanar ɗaure Yari da Fintiri?

Yari da Fintiri
Bayanan hoto, Abdulaziz Yari da Ahmadu Fintiri na fuskantar bincike kan zargin karya ka'idar tashar jirgin sama

Ministan sufuri na Najeriya Hadi Sirika, ya yi barazanar gurfanar da gwamnan Adamawa da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul-aziz Yari gaban kuliya, muddin aka same su da laifin karya dokokin da aka gindaya a tashoshin jiragen saman kasar.

Ministan ya yi wannan barazanar ne a yayin taron da kwamitin ko ta kwana na shugaban kasa akan cutar korona wanda ake gudanarwa a kullum.

Ministan ya ce ba za su saurarawa duk wanda ya saba doka ba komai girmansa.

Hadi Sirika ya ce sun karbi korafi kan zargin yadda wasu mutane ciki harda manya ke karya dokoki.

Ministan a cikin kakkausan harshe ya ce suna bincike kuma idan aka same su da laifi za su iya fuskantar ''hukuncin dauri daga wata biyu zuwa shekara 10, ko a ci su tara ko kuma a hada masu hukunci biyu''.

Wadannan kalamai na ministan na zuwa ne bayan hukumar sufurin jiragen sama ta kasa, FAAN ta yi zargin Gwamna Fintiri, da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, na karya ka'idojin filin jirgin sama.

Ko da yake manyan mutanen biyu sun musanta wadanan zarge-zarge.

Sai dai kuma Sirika ya ce idan har bincike ya tabbatar da cewa sun yi laifi za a hukunta su, amma idan ba su karya doka ba kamar yadda FAAN ta zarge su, to za a nemi afuwarsu a bainar jama'a.

''Wannan zargi kan fasinjoji ya hada da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda a ranar (Laraba) muka kwashe tsawon lokaci muna tattaunawa da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri.

''Abdulaziz ya je Kano a ranar Asabar, shi kuma Fintiri ya je Fatakwal sannan Chief Nduka Obigbene a nan Abuja ake zargin ya karya ka'ida,'' in ji Sirika.

A cewar ministan bisa dokokin sufurin jiragen sama, akwai hukunci da aka tanadarwa fasinja da ya nuna rashin da'a.

Hadi ya nuna takaicinsa kuma ya lashi takobin cewa duk fasinjoji da ke nuna rashin da'a ko saboda mukami ko matsayi abu mai sauki da za a yi shi ne hada su da hukumar 'yan sanda, kuma wajibi ne a hukunta ko waye bisa sharuddan doka.

Ministan ya kuma ja hankalin fasinjoji da su mutunta kansu da umarni saboda kaucewa shiga barazana ko abin kunya.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Me ake zargin su da shi?

Tun bayan gabatar da korafin da FAAN ta yi ake ta kumfar-baki tsakanin wadanda ke ganin ana bai wa wasu tsirarun mutane damar karya doka saboda mukami ko girman matsayinsu.

An shafe kwananki ana ce-ce-ku-ce abin da ya kai ga shugaban kwamitin harkokin sufurin jiragen sama a majalisar wakilai, Nnolim Nnaji jaddada muhimmanci ma'aikan tsaro da jami'an lafiya su cire tsoro wajen aiwatar da ayyukansu ba tare da nuna fargabar wani na da muhimmanci ko mukamin gwamnati ba.

A nasa bangaren dai tsohon gwamnan Zamfara Yari ya ce zargin da FAAN ta yi masa cewa ya hankada daya daga cikin ma'aikatanta kuma ya ki bin umarninsu a filin jirgin sama na Kano karya aka yi masa.

A wata sanarwar da ya fitar ta hannun mai taimaka masa ta kafar yada labarai, Mayowa Oluwabiyi ya shaida wa BBC cewa gwamnan ya bukaci a nemi afuwarsa kan sanarwar da suka fitar saboda a matsayinsa na mai mutunci ba aikata wannan laifi ba.

FAAN ta ce gwamnan ya ki yadda a auna zafin jikinsa ko ya wanke hannu da kuma yi wa jakarsa feshi kamar yadda aka gindaya sharuddan saboda annobar korona.

Mutum na biyu da FAAN ta zarga shi ne gwamnan Ahmadu Fintiri na Adamawa da tace shi da tawagarsa sun yi biris da umarnin goge hannunsu da sinadarin sanitiza, haka zalika bai amince a yi wa jakarsa feshi ba.

Zargin da daraktan yadda labaran gwamnan, Solomon Kumangar ya musanta.

Zai yiwu a daure su?

Minista Hadi Sirika dai ya ce tabbasa idan an kama su da laifin za su fuskanci hukunci watakila har da na dauri.

Sai dai hakan ka iya zama mai wahalar aiwatarwa a kan Gwamna Fintiri na Adamawa saboda a kundin tsarin kasa gwamnoni na da kariya ta musamman da ba zai yiwu a daure su a yayin da suke kan mukami ba.

Amma ga Abdul'aziz Yari, a baya-bayan nan an ga yadda shari'a ta daure wasu tsofaffin gwamnoni kan kama su da wasu laifukan daban da irin wannan. Don haka watakila hukuncin na iya hawa kansa idan har an tabbatar.

Wannan layi ne

Wasu karin labarai da zaku so karantawa:

Wannan layi ne