Hotuna: Yadda Joshua Dariye ya rika kuka a kotu

An shafe sama da sa'o'i shida ana karanta shari'ar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye.

Joshua Dariye
Bayanan hoto, Joshua Dariye ya kasance cikin damuwa da dimuwa a lokacin da ake masa shari'a
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Sau biyu gwamnan ya ziyarci ban-daki domin kama ruwa
Dariye

Asalin hoton, Facebook/EFCC

Bayanan hoto, Mista Dariye shi ne tsohon gwamnan Filato daga shekarar 1999 zuwa 2007
Dariye

Asalin hoton, Facebook/EFCC

Bayanan hoto, Tsohon gwamnan ya rika kuka lokacin zaman kotun
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Mai Shari'a Adebukola Bamijoko ta ce ta yanke ma sa daurin shekara 14 bayan ta same shi da laifin cin amana da halatta kudin haram
Joshua dariye
Bayanan hoto, Bayan an yanke masa hukunci, jami'an hukumar EFCC ne suka fito da shi domin kai shi gidan kaso
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Tsohon gwamnan na Filato ya nuna rashin amincewa a dauke shi cikin a-kori-kurar da jami'an EFCC suka kawo, kuma wasu daga cikin mutanensa sun ce hakan bai dace ba.
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Sai dai kuma jami'an EFCC ba su sauya motar ba.
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Sun saka sanatan mai wakiltar Filato ta tsakiya a cikin a-kori-kurar, sannan suka fice da shi.
Joshua Dariye
Bayanan hoto, Daure Joshua Dariye ya zo makwanni bayan mai shari'a Adebukola Bamijoko ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame hukuncin daurin shekara 14