Buhari ya ja kunnen ministocinsa a kan raina majalisa

@NGRPRESIDENCY

Asalin hoton, @NGRPRESIDENCY

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi ministoci da manyan jami'an hukumomin gwamnatinsa su kyautata alaƙa da majalisar tarayyar Najeriya.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkar yaɗa labaran shugaban, Garba Shehu ya fitar ta ambaton Buhari na cewa ba zai lamunci duk wani rashin mutunci ga majalisa daga duk wani jami'in ɓangaren zartarwa ba.

Ta ce shugaban ya yi wannan jan kunne ne lokacin da yake ganawa da shugabancin majalisun tarayya a jiya Alhamis, inda suka tattauna game da wasu ayyukan baya-bayan nan na majalisa.

Rahotanni sun ce jan kunnen na zuwa ne sa'o'i bayan shugaban hukumar raya yankin Neja Delta, Daniel Pondei ya fice daga zauren sauraron jin bahasi game da bincike kan harkokin kuɗin hukumar.

Jami'an hukumar dai sun zargi shugaban kwamitin binciken na majalisar wakilai da cin hanci, inda suka ce za su ci gaba da halartar zaman ne kawai idan ya janye jiki daga bincike.

Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan dambarwar da ta sanya majalisar dakatar da wani shirin ɗaukar matasa 774,000 aikin wucin gadi, sakamakon taƙaddama da ministan ƙwadago.

Sanarwar fadar shugaban ƙasa ta umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati su tafi da harkokinsu ta yadda ba za su yi zagon ƙasa ga majalisa da shugabancinta gami da wakilanta ba.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani a kan ko gargaɗin na Buhari na nufin minista Festus Keyamo zai ba da kai ga buƙatar majalisar ba, game da batun ɗaukar dubban matasan ƙasar aikin wucin gadi.