Boko Haram: Sojin Najeriya sun yi babban kamu

Asalin hoton, @HQNigerianArmy
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wasu manyan mayakan Boko Haram guda 10 a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin kasar.
Sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce cikin wadanda ta kama har da babban direban kungiyar Alhaji Bukar Modu da aka fi sani da sunan Modu China.
Ta ce Modu China shi ne mai lamba 89 a cikin jerin sunayen mayakan Boko Haram da take nema ruwa a jallo.
Rundunar sojin ta ce ta kama mayakan ne a samamen da ta kai a ranar Talata 9 ga watan Oktoba kuma ta kama su ne a Pulka cikin jihar Borno.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Tun a ranar Litinin rundunar sojin ta ce ta kama wasu mutum takwas da take zargi 'yan Boko Haram ne a Mainok a samamen da ta kaddamar na kakkabe Boko Haram a babbar hanyar Maiduguri-Damaturu-Bama.
Ta kuma ce ta ceto fararen hula 12 da mayakan Boko Haram ke garkuwa da su da suka kunshi mata da kananan yara.







