Ebola: Bazuwar da cutar ke daɗa yi na sanya damuwa

Asalin hoton, AFP
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta damu game da ɓarkewar cutar ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, wadda ta zama mafi yawa da aka taɓa samu a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
An ba da rahoto mutum 56 ne suka kamu da cutar a lardin Equateau na Jamhuriyar Kongo tun bayan ɓullarta a watan Yuni.
Daraktar Hukumar Lafiyar a nahiyar Afirka, Dr Matshidiso Moeti ta ce "Wannan babban abin damuwa ne, musammam ma ganin cutar ta zarce yawan da aka taɓa samu a wannan yanki, wanda aka killace shi lokacin mutanen da cutar kama ba su wuce 54 ba.
A cewarta, wasu daga cikin mutanen da suka kamu na zaune ne a can yankuna masu nisa da ke zagaye da dazuka, abin da sanya buƙatar ƙarin ƙwazo da kayan aiki don kai ɗauki.
Jami'ar lafiyar ta ce an koyi darussa a lokacin ɓarkewar cutar cikin wannan yanki baya a shekara ta 2018, lamarin da ya sa aka yi wa mutane sama da dubu goma sha biyu allurar riga-kafi a tsawon mako shida.
A cikin watan Yuni ne, hukumomin lafiya suka ayyana kawo ƙarshen ɓarkewar cutar mafi muni a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.
Cutar ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu biyu da ɗari biyu cikin lardunan arewa maso gabashin ƙasar uku.







