Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Nijar: Jam'iyyu 10 da ke shirin fafatawa
A ranar 27 ga watan Disamba ake saran al'umma Nijar su kada kuri'a a zaben shugabancin kasar da na 'yan majalisar dokoki da kuma kananan hukumomi.
Jam'iyun kusan 150 ne za su fafata a zabukan da hukumar zaben kasar ta CENI za ta shirya dan zaben wanda zai maye gurbin shugaba Mahamadou Issoufou da kuma mashawarta matakin jihohi da na kananan hukumomi.
A yayinda zaben ke dada karatowa 'yan siayasa kasar musamman bangaren masu adawa na bayyana shakku kan yadda hukumar zaben ke tafiyar da ayyukanta na shirye-shiryen zaben.
Kawo yanzu dai 'yan siyasa kalilan ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin tutar jam'iyyu daban-daban.
A yanzu dai kusan jam'iyyun siyasa masu mulki da na adawa 10 ne suka tsaida 'yan takara a zaben shugabancin kasar.
Jam'iyya mai milki ta PNDS Tarraya ta tsaida dan takararta, Bazoum Mohamed tsohon ministan cikin gida a matsayin wanda zai daga tutarta a zaben na shugaban kasa.
Jam'iyar MNSD Nasara ta tsahon shugaban kasar Tanja mahamadou a nata bangare ta tsaida Seini Oumarou wanda yanzu ke rike da mukamin wakili na musaman na shugaban kasa.
Ita kuma jam'iyar MPR Jamhuriya ta tsaida shugabanta Alhaji Albade Abouba.
Bangaren adawa kuma jam'iyar madugun adawa kasar ta Moden FA Lumana ta tsaida Hama Amadou shugaban jam'iyar tsohon Firaministan kasar, tsohon kakakin majalisar dokoki duk da haramcin da ke kanshi na zabe ko tsayawa takara, sakamakon hukuncin zaman gidan yarin da wata kotu da ke Yamai ta yanke a kan sa kan laifin safarar jarirai.
Jam'iyar MPN Kishin Kasa ta tsaida, Ibrahim Yacouba a matsayin dan takararta. Sai tsohon shugaban kasar Mahamane Ousmane da jam'iyar shi ta canji ta bashi takara.
Jam'iyar Dubara ta tsohon shugaban mulkin sojin General Salou Djibo itama ta bayyana nata dan takara da zai kare mata tuta a zaben na 2020.
Jam'iyar na daya daga cikin sabbin jam'iyyun da a karon farko suka tsaida su 'yan takara.
A shekarar 2011 ne aka zabi shugaba Mahamadou Issoufou da ya kawo karshen rikon kwaryar mulkin soji bayan da suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Tanja Mahamadou.