Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 7,000 'sun tsere daga sansanin 'yan gudun hijira a Nijar'
Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce mutane sama da dubu bakwai sun tsere daga matsugunansu a Jamhuriyyar Nijar, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a wani yankin da aka tsugunar da 'yan gudun hijirar kasar Mali da kuma 'yan Nijar wadanda tashin hankali na cikin gida ya raba da muhallansu.
Da ma mutane sama da dubu talatin da biyar ne ke samun mafaka a yankin na Itikane da ke jihar Tahoua.
Galibin wadanda suka tseren 'yan gudun hijira ne 'yan kasar Mali.
Wani mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Nijar, Jean Sebastien Josset ya shaida wa BBC cewa yanzu dubban mutanen da suka tsere na wani matsuguni na wucin gadi kusa da garin Telemce, kimanin kilomita 27 daga inda aka kai harin.
Jami'in hukumar ta UNHCR ya ce mutanen na matukar bukatar muhimman kayayyakin rayuwa, kamar ruwa da abinci da kuma kayayyakin kiwon lafiya.
Mr Jean Sebastien Josset ya ce da dama daga cikinsu wadanda suka hada da mata da kananan yara sun gigita sakamakon harin, amma kungiyoyin agaji da hukumomin kasar na kokarin tallafa masu.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana harin da ya raba dumbin mutanen da matsugunansu a matsayin na mugunta, wanda kuma babu kalmar da za ta iya bayyana iya muninsa.
Shugabannin 'yan gudun hijira biyu da kuma wani shugaban al'umma ne dai suka rasa rayukansu a harin da masu tayar da kayar baya suka kai yankin Itikane da ke jihar Tahoua ta jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi.
Masu tayar da kayar bayan sun kuma kona kayayyakin abinci da lalata na'urar babbar cibiyar da 'yan gudun hijirar ke samun ruwan sha da kuma hasumiyoyin wayoyin sadarwa na salula.
Sakamakon harin, yanzu dai dubban 'yan gudun hijirar kusan sun gudu gara ne suka fada gidan zago, domin irin tashin hankalin da tun farko ya kore su daga Mali wasu kuma daga yankunansu a cikin Nijar, sun sake gamuwa da shi.
A 'yan watannin nan dai, ana fuskantar karuwar hare-hare kan al'umomi da ke yankunan iyakokin Mali da Nijar da kuma Burnika Faso inda masu tayar da kayar baya masu alaka da IS da Alqaeda ke aika-aika.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce jama'ar yankunan na fargabar samun karin hare-hare, kuma tabarbarewar tsaron na kara raba 'yan gudun hijira da inda suka samu mafaka.
To sai dai kuma Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR na cewa duk da cewa matsalar tashin hankalin na takaita damar kai taimakon jin kai ga masu bukata, to amma fa ita da wasu kungiyoyin agaji na kara kaimi.
Tana kuma kukutawa wajen taimaka wa ta fuskar samar da ilmi da matsuguni da kuma magance matsalar lalata da cin zarafin mata da kuma kiwon lafiya da abinci.