Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kanye West: Fitaccen mawaƙi zai tsaya takarar shugaban Amurka
Lokacin karatu: Minti 1
Fitaccen mawakin nan Ba'amurke mai salon rap Kanye West ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.
A wani sakon Twitter, West ya ce lokaci ya yi na cika alkawarin Amurka.
Wannan sanarwa ta Kanye West nan da nan ta samu goyon bayan hamshakin mai kudin nan Elon Musk.
An san Kanye West a matsayin aboki ga Donald Trump - kuma matarsa ita ma mawakiya Kim Kardashian ta ziyarci fadar White House lokuta da dama domin tattauna batun sake fasalta gidajen yari.