Coronavirus: Donald Trump ya sanya takunkumi bainar jama'a

Asalin hoton, Reuters
Shubaban Amurka Donald Trump ya saka takunkumi a karon farko tun barkewar annobar korona.
An ga shugaban sanye da takunkumi ne lokacin da ya ziyarci wani asibitin soja da Washington inda ya gana da sojojin da suka ji rauni da kuma ma'aikatan lafiya.
"Ban taba adawa da saka takunkumi ba amma nasan akwai lokaci da kuma wurin da ya dace," a cewar Trump bayan ya fice zuwa Fadar White House.
A baya shugaban ya taba cewa ba zai taba sanya takunkumi inda ya yi shagube ga abokin hamayyarsa Joe Biden saboda ya sa takunkumi.
Amma a ranar Asabar ya ce "Ina ganin idan kana asibiti, musamman a wani yanayi, inda zaka yi magana a gaban sojoji da mutane da dama, ina ganin ya fi dacewa ka saka takunkumi."
A wata hirarsa da kafar Fox a makon da ya gabata, Mista Trump ya nuna cewa takunkumi ba nasa ba ne inda ya kwatanta kansa da Lone Ranger labarin wani gwarzo da wani abokinsa Amurkawa da suka yi yakin da ake kira American Old West
Amma lokacin da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a watan Afrilu ta fara shawartar mutane su dinga rufe hanci a bainar jama'a domin dakile bazuwar cutar, a lokacin Mista Trump cewa ya yi ba zai bi umurnin ba.
"Ban yi tunanin zan iya saka wa, a cewarsa a lokacin. "Sanya takunkumi yayin da nake magana da shugabanni da Firaministoci da sarakuna - ban ga yiyuwar haka ba."
Wasu rahotanni na kafafen yada labarai sun ce masu taimakawa wa shugaban sun sha fada masa cewa ya dinga saka takunkumi.
Wane hali ake ciki yanzu haka a Amurka?
Cikin sa'a 24 mutum 66,528 suka kamu da cutar korona, kuma yanzu cutar ta kashe mutum 135,000 tun bullarta, a cewar alkalumman Jami'ar Johns Hopkins
Louisiana ta kasance jiha ta baya-bayan nan da ta tilasta saka takunkumi a bainar jama'a.
Gwamnan jihar dan jam'iyyar Democrats John Bel Edwards ya bayar da umurnin rufe wuraren shan barasa da takaita bude wuraren cin abinci inda aka hana mutane zuwa cin abinci. Kuma sabbin matakan za su fara aiki ne daga ranar Litinin.
Ana tunanin 'yan majalisar jihar daga bangaren 'yan Republican za su kalubalanci matakin.
Makwabciyarta Texas an sake samun mutum 10,500 da suka kamu da cutar a ranar Asabar.
Gwamnan South Carolina ya bayar da umurnin haramta sayar da giya bayan karfe 11:00 na dare domin rage bazuwar cutar korona.











